Connect with us

KASASHEN WAJE

Coronavirus Ta Kama Dan Najeriya A Amurka

Published

on

Hukumomin birnin Washington DC da ke Amurka sun ce, wani dan Najeriya da ya ziyarci kasar ya kamu da cutar Coronavirus kamar yadda gwajin da aka yi masa a wani asibiti da ke Maryland ya nuna.

Mai rike da kujerar Magajin Garin birnin , Muriel Bowser ta ce mutumin ya dauki lokaci a Washington bayan ziyarar da ya kai daga Najeriya inda yake zaune da yan uwansa.

Jamiar ta ce, sun tabbatar da kamuwar mutane biyu a Washington, wato dan Najeriyar da kuma wani mazaunin birnin.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce, babu alamar cewa, dan wasan ya kamu da kwayar cutar ce daga Najeriya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: