Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Gombe Ta Kashe Biliyan Bakawai Don Gina Garejin Mota

Published

on

Gwamnatin jihar Gombe ta kashe sama da naira biliyan bakwai da shirin sake kashe sama da naira biliyan biyu wa ginin filin adana motoci ta Mega Motor Park, Tankers Bay da kuma babban dakin taro na kasa da kasa da ke Gomben hadi da wasu wuraren da gwamnatin baya ta wofintar.

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, shine ya shaida hakan a jiya lokacin da ke amsar rahoton kwamitin da ya kafa na gina garejin ajiyan motoci ta ‘Mega Park’, Tankers Bay da kuma cibiyar dakin taro ta International Conference Centre da ke Gombe, kamar yanda wata kwafin sanarwar manema labaru da Ismaila Uba Misilli, babban mai taimaka wa gwamnan jihar kan hulda da ‘yan jarida ya fitar a jiya.

Gwamnan ya shaida cewar kawo yanzu gwamnatin jihar ta kashe sama da naira biliyan bakwai 7 don gina filin adana motoci ta Gombe Mega Motor Park, Tankers Bay da dakin taro na kasa da kasa International Conference Centre da ke Gombe, yana mai karawa da cewa yanzu haka gwamnatin jihar za ta sake kashe wasu naira biliyan hudu 4b domin tabbatar da kammala aiyukan domin a samu zarafin amfani da su yanda ya kamata.

Gwamna Inuwa ya kuma ce, an samu sauye-sauye da canje-canje masu ma’ana a karkashin gwamnatinsa da ke kyautata rayuwar al’umma kai tsaye. Ya ce, babu wasu aiyukan da aka yi watsi da su da zai kyale haka nan ba tare da gwamnati ta kammalasu ko tabbatar da maidasu ga musu amfani wa jama’a ba.

A cewar gwamnan tabbatar da kyautata manyan aiyukan raya jihar ne ya sanya a gaba, a bisa haka ne ya ce gwamnatin za ta kammala dukkanin aiyukan da aka yi watsi da su da tabbatar da sun amfani jama’a yanda ya kamata.

A cewar gwamnan kwamitin da ya kafan ya zama dole lura da muradun gwamnatin na tabbatar da cewar dukkanin wani sisi da kwabon da gwamnati ta fitar ya zama an fitar da shi ne ta hanyar da ta dace domin ci gaban jihar.

Ya baiwa jama’an jihar Gombe tabbacin gwamnatinsa na yin duk mai iyuwa domin kammala aiyukan cikin hanzari domin amfanan jama’an jihar.

Shugaban kwamitin Dakta Manassah Daniel Jatau, wanda kuma shine mataimakin gwamnan jihar, ya shaida cewar kwamitin ya gano yanda gwamnatin baya ta kara yawan kudaden kwangilar daga adadin da aka ware tun da farko, sai ya nuna mamakinsa a kan hakan.

“Abin mamaki ne yanda wasu daga cikin aiyukan nan suka yi tashin gwauron zabi ba tare da gamsassun dalilai ba; misali, International Conference Centre ‘ICC’ daga fari naira biliyan 2.2 ya zo ya karu zuwa biliyan 4.2, aikin filin adana motoci na zamani ta Mega Park daga biliyan 3.2 ya haura zuwa biliyan 6 daga bisani, haka zalika aiki aikin filin Tanker Parkin Bay daga naira miliyan 352 ya koma zuwa naira miliyan 565,”

Dakta Jatau ya lura da cewar kafa kwamitin da gwamnan yayi ya kara tabbatar wa jama’an jihar irin kishisa da son yin gaskiya da adalcin gwamnan ne hadi da tabbatar da dakile barnatar da dukiyar jama’an jihar haka siddan.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: