Connect with us

TATTAUNAWA

Kafin Zaben 2023 ZA A Daina Taka Mata A Harkokin Siyasa – Zara

Published

on

HAJIYA ZARAH I. ABDULLAHI ita ce shugabar gidauniyar Zarah Arthur Foundation. A zantawarta da Wakilin LEADERSHIP A YAU, MUHAMMAD AWWAL UMAR, kan ranar mata ta duniya da a ka gudana ranar Lahadin da ta gabata, ta yi tsokaci kan matakan da su ke dauka na wayar da kan mata a harkokin gwamnati da siyasa da kuma yunkurinta na wayar da kan mata.  Ga dai yadda takaitacciyar hirar ta kasance:

 

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 8 ga Maris na kowacce shekara, don tunawa da mata da kuma tattauna matsalolin da su ke fuskanta. Wane karin haske za ki yi?

Da farko ina godiya ga Allah kuma ina taya ‘yan uwana mata murnar wannan rana. Sannan ina godiya ga uwargidan gwamnan Neja kan rawar da take takawa a bangaren cigaban harkokin mata a jihar Neja.

Amma ban tsaya nan ba, a gaskiya mata an mayar da mu rijiyar yasa, domin idan ka duba a bangaren siyasa muke da kashi saba’in da biyar na kowace irin siyasa amma da zaran an cin ma nasara mu ake mayarwa baya, a wannan karon mun kuduri aniyar hada kan matan kasar nan a kowani bangaren siyasa da harkokin gwamnati, domin kafin shekarar 2023 muna fatar mata zasu fito a fafata da su a harkokin zabe daga yin takara har zuwa zabe domin mun kusa daina zama ‘yan rakiya kamar yadda aka dauke mu a baya.

Idan ka duba a na dan samun canje canje a yanzu, domin idan zamu samu iyaye kamar matar gwamnan Neja, Dakta Amina Abubakar Sani Bello lallai za a samu canji mai alfanu.

 

Yanzu wane shiri ki ke yi, don ganin wannan mafarkin naki ya zama gaskiya?

Yanzu a karkashin gidauniyar mu ta Zarah Arthur Foundation, mun yi hadin guiwa da wata kungiya daga kasar Ghana, muradin mu abu hudu ne, ilmantar da mata, horar da matan da suka rasa mazajensu ta fuskar dogaro da kai, horar da matan aure da ke kulle a gidajen aure hanyar da zasu dogara da kan su ba tare da jiran maigida akan harkokin yau da kullun dari bisa dari ba, na karshe kulawa da wasu makarantun allo dan daukar dawainiyar almajirai ta fuskar ciyar wa da koyar da su karatun boko, wannan muna fatar kammala shi cikin shekaru hudu ne.

 

Amma ki na ganin a dan wannan lokacin gidauniyar ki za ta iya cin ma wannan burin?

Kwarai kuwa, domin mun gudanar da shirye shirye a baya a karkashin Zarah Stars Foundation wanda a Neja ne kawai ya tsaya, amma yanzu tafiyar ta kasa ce gaba daya, shi yasa muka gayyato mata kwararru a fagen siyasa daga nahiyar Afrika dan mu hada hannu mu yi aiki tare, ka ga a baya muke tallata ‘yan siyasa wanda da zaran sun dare sai su bar mu a rabon omon wanki da sabulun man shafawa, yanzu kuma mu be zamu tallata kan mu da kan mu, mu din ne za mu yi sana’a mu nemi kudin kuma yi abinda ya kamata da su, kan haka za mu watsu a duk wani bangaren da kan san maza na fadawa dan nema da kuma jajircewa wajen yiwa kasa aiki da abinda muka samu, za mu tabbatar kafin 2023 din nan mata sun ilmantu sun iya sana’a ta yadda za a yi gwagwarmaya da mu a kowani bangaren.

 

A Arewa maganar addini na da muhimmanci. Kan haka ba lallai ne mata su samu karbuwa ba. Ya za ku bullo wa matsalar?

Gaskiya ne, amma babu addinin da yace mace ta kwanta ko, shin suwa ke bada tarbiya a matakin farko na yaro, ina ce mata ne ai. Idan mace ba ta da ilimi ya rayuwar yake kasancewa. Saboda idan mata suka samu ilimi komai na rayuwa zai tafi yadda ta kamata domin mu mata mu ne malaman farko na rayuwar dan Adam, ashe kenan idan za mu iya rike gida yai kyau ba inda ba za mu iya rikewa ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: