Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gidauniyar Badamasi Burji Ta Kammala Gina Makaranta Da Daukar Nauyin Karatun Daliban

Published

on

Batun samar da ingantaccen ilimi, harka ce da a ke bukatar hada hannu, domin samarwa da al’umma ingantaccen ilimi, wanda a halin yanzu da yawa aka zuba wa gwamnati ido wajen daukar nauyin dukkanin harkokin ilimin a kowane mataki. Hakan ta sa a ke fatan samun shigowar al’umma wajen bayar da gudunmawa wajen hada hannu da gwamnati, domin rungumar harkokin ilimi.

Al’ummar garin Burji da ke Karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano, tasu layar ta yi kyan rufi, domin Allah Ya albarkaci garin da wani dan kishin kasa da al’ummar mahaifarsa, Alhaji Badamasi Shu’aibu Burji, Shugaban Kamfanin Centaury Research, wanda ke buga Jaridar Concern da Kuma Adala, wanda a halin yanzu an yi ittifakin daya da daya wannan bawan Allah ya zarce sa’a wajen sauke wa al’ummar mahaifarsa kabakin arzi’ki, musamman ta fuskar ilimi.

Ranar Lahadin da ta gabata ne, aka gudanar da bitar sanin makamar aiki ga wasu Malamai guda 34 da suke koyarawa a makarantar da Gidauniyar Badamasi Burji ta gina a garin na Burji, wanda aka gudanar a harabar makaranta da ke garin na Burji. Wannan makaranta ce, wadda ya gina ta shi kadai tare da taimakon Ubangji, an samar da makarantar Islamiyya da ilimin zamani, wanda ake karatu da safe, yamma da kuma dare. Bayan haka, kuma gidauniyar ta gina makarantar Sakandire wanda yanzu aikin gaf ya ke da kammaluwa, domin fara gudanar da karatu a cikinta.

Wannan bawan Allah, saboda kokarin da yake na ganin al’ummar Karkara sun samu ilimin kamar yadda ya kamata, ya yi kokarin kawo tsangayar Jami’ar NOUN cikin wannan gari, domin samun matsuguni da za a cigaba da aiwatar da harkokin karatu ga wanda ya samu damar zuwa matakin Jami’a a harkar ilimi. Yanzu haka, ya samar da katafaren fili tare da jibge kayan aiki domin fara aikin wannan tsangayar Jami’ar NOUN.

Wani abin sha’awa ga al’amarin wannan mutum shi ne, yanzu haka akwai yara da ke karatu a wannan makaranta da suka tasamma dubu biyar, amma za a yi mamakin dukkan wadanann yara shike ba su kayan makaranta, kayan karatu tare da samar masu da dukkan wani abu da ake bukata wajen kyautata tsarin neman ilimi, wanda ya dace da duk wani tsarin karatu da ake da shi.

Badamasi Shu’aibi Burji, ya yi la’akari da muhimmancin samar da sana’o’in dogaro da kai ga mata da Matasa, wannan tasa a dai wannan makaranta ya ware wani bangare da a ka tanadi kayayyakin koyar da sana’o’in, wanda suka hada da sana’ar dinki, saka, man sabulu da sauran kananan sana’o’i wadanda mata kan iya yi a cikin gidajen aure, domin taimakawa harkokin gida na yau da kullum. Sannan kuma, dukkan kayan da ake koyar da sana’o’in, shi ya tanadarwa masu koyon sana’ar, idan an sana’anta kuma shike nemo masu saye domin samun damar shigar da kayan da a ka sarrafa cikin kasuwanni.

An shirya gudanar da wannan taron bita, don kara zaburar da malaman domin sanin makamar aiki tare da inganta aikin nasu. A lokacin gudanar da bitar, malamai guda 36, guda 16 su ne Malaman Boko sai kuma 18 wadanda ke koyar da harkokin Addinin Islama, kuma daga cikin wannan adadi na Malamai, shida ne kadai na Gwamnati, amma sauran duk wannan bawan Allah ke ba su abin sawa a bakin salati duk karshen wata.

Da ya ke yi wa mahalarta taron bitar karin haske, Malam Alhasan Musa wanda kuma shi ne jagoran masu horar da Malaman, ya bukaci Malaman da su kara jajircewa tare da sadaukar da kai, domin ba wanda zai biya su wannan aiki sai Allah, daga nan sai ya nuna farin cikinsa tare da yi wa Allah godiya bisa ba su wannan jajirtaccen dan kishin kasa da al’umma, bisa wannan kabakin arziki da ya ke saukewa wanna yanki, ya ce haka ya kamata duk wani wanda Allah ya horewa ya yi, domin bunkasa cigaban al’ummarsa.

“Ku sani duk wani taku guda da ka yi lahira ka ke tunkara, saboda haka shin ko kana yi wa wannan mahanga kyakkyawan tanadi?”

Daga nan ne kuma, sai Shugaban Gidauniyar ta Badamasi Burji ya jagoranci kaddamar da sabon kayan makaranta, domin daliban Nazire wanda ake dauka a halin yanzu, inda ake baiwa kowanne dalibi kayan makaranta da kayan karatu, haka kuma an raba jakakkuna da kayan rubutu ga mahalarta taron bitar wanda aka gudanar.

Da ya ke gabatar da jawabinsa ga dandazon al’ummar da suka yi dafifi domin nuna godiyarsu ga wannan abin alhairi, Alhaji Badamasi Shu’aibu Burji, ya bayyana cewa, yin wannan aiki a wurinsa wajibi ne, domin nan ce mahaifata kuma ba ni da garin da wuce garin Burji a rayuwata, saboda haka nake fatan ganin al’ummarmu sun samu ilimi gwargwadon iko tare da samun sana’o’in da za su dogara da kansu. Ina kara godiya ga ‘yan’uwa wadanda suke aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da ganin wannan aiki an samu nasara.

Haka zalika, Burji ya godewa Abokai da Aminai wadanda suka yi tattaki har garin Burji, domin taya shi murnar wannan aikin alhairi da muke fatan Allah ya kare mu da karfin guiwar cigaba da wannan hidima, na sani wannan ba wayo na ba ne abu ne daga Allah kuma ina kara yi wa Allah godiya kwarai da gaske.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: