Connect with us

MAKALAR YAU

Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Duniya Ta Na Kallon Ka (5)

Published

on

Yau ma kamar kowane mako, cikin ikon Allah na dawo inda na ke sa ran kammala wannan rubutu nawa mai dogon zango, wanda ya dauki ne kusan makonni biyar Ina yin sa a kan matsalar tsaro.

To, amma kafin karkare wannan rubutu nawa, na yi alkawarin kawo wasu daga cikin maganganun shugaba Muhammadu Buhari dangane da wannan tirka-tirka ta matsalar tsaro wanda ga alamu gwamnatinsa na kan hanyar barin mummunan tarihi na kasa maganin wannan matsala da ya ce zai gama da ita ba tare da daukar wani lokaci ba.

Abubuwan da su ka rika biyo bayan kai hare-haren wuce gona da irin da ‘yan ta’ada ke kaiwa, abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin wannan gwamnati ba, musamman ikirarin da ta yi na cewa wannan matsala sunanta warkaka da zaran ya dare madafar iko, ashe abin ba haka yake, an dafa kaza an bai mai ta kai!

Babu shakka idan a ka ce maganganu ne ke kawar da batun ta’adancin a kasar nan, da gwamnatin shugaba Buhari ta yi na daya wajan wannan bangare, to amma da ya ke ba haka abin yake ba, gashi yanzu tana neman yin na daya wajan gazawa da samarwa da jama’a yanayin da za su yi barci da ido rufe.

A makon da ya gabata na kawo wasu maganganu da shelkwatar rundunar Sojojin Najeriya suka yi dangane da batun kai hare-hare da kungiyar Boko Haram da ‘yan bindiga ke yi a arewacin Najeriya, inda har gobe rundunar tana da kwarin gwiwar cewa zata yi maganin wadannan mutune amma fa da baki.

Abinda yasa na ce da baki shi ne, maganar yin amfani da makami ko dibarun yaki, gaksiyar magana hakan ta gagara kawar da wadannan mutane, tun ana da fatan cewa hakan na iya faruwa har an hakura da faruwan hakan a karkashin wannan gwamnati.

Idan ba a manta ba, na tsaya ne a daidai inda nake maganar wasu kalamai da shugaba Buhari ya yi jim kadan bayan kai harin da ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna inda suka yi kisan kare dangi suka ci karansu babu babaka ba tare da jami’an tsaro sun fuskance su ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun dauki lokacin suna kisan kiyashi ba tare da wasu jami’an tsaro sun kawo dauki ba, lamarin da ake gani tamkar fitowa a fili ne, ana nunuwa duniya cewa wannan gwamnatin karkashin jagoranci shugaba Buhari ba zata iya ba.

Bari mu ji abinda ya fada bayan kai harin, mu ji cewa maganganun na shi, sun da ce da wannan yanayi na kai hari, ma’ana suna dauke da tausayawa ko kara daukar alwashin ganin karshen ‘yan ta’ada a yankin arewa inda nan ne shugaba Buhari ya fito?

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadi da bakin cikin yadda ‘yan bindiga suka kashe mutane 51 a karamar hukumar Igabi, cikin jihar Kaduna ba tare da an kai farmaki daga bangaran jami’an tsaro cikin sauri ba.

Kamar yadda rahotanni suka nuna mahara sun yi wannan mummunan kisa a ranar wata Lahadi, inda suka kai mummuman farmaki a kan mazauna yankin Kerawa da wasu kauyuka hudu.

Jaridun Najeriya da kuma na kasashen waje sun ruwaito labarin yadda ‘yan bindigar suka karkashe manya da kananan yara, jira-jirai da almajirai da sauran jama’a.

Sai dai shugaba Buhari ya ce, “Gwamnati ba za ta mika wuya ga mahara ba, domin su abinda suke so sojoji su daina kai musu hari.

“Ba za a daina fatattakar su ba. Domin rahoton da na samu an ce min, ‘yan bindiga na jin haushin yadda sojoji da ‘yan sanda ke yawan kai musu farmaki sosai a sansaninsu da ke cikin dazuzuka.

A cikin wata sanarwa da kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya gargadi ‘yan bindiga cewa su bar ganin su na kashe mutane, to akwai ranar-kin-dillanci.

Ya ce gwamnatinsa tana bakin kokari don tabbatar da nasarar murkushe ‘yan bindiga kakaf da suka addabi Najeriya musamman yankin arewa.

Wannan ke nan, dangane da abinda ya faru a jihar Kaduna kwanakin baya, to sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, idan muka duba wadannan maganganu sai mu ga kamar ba nan bane muhalinsu ba, domin har aka fara magana a kareta babu inda aka yi masu jaje.

Maganar jaje wani abu ne da za a iya cewa wannan gwamnatin ta shugaba Buhari ta daina yin sa, sai dai kawai ace barazana ko asa Garba shehu ya fitar da sanarwa, da kurin cewa za aga bayan ‘yan ta’ada, alhali babu wani shiri na yin haka.

Akwai maganganu na tausayawa da yakamata shugaba ya yi idan an samu kuskuran faruwar irin wannan al’amari da fatan kadda Allah ya maimaita irinsa, saboda haka a lokacin da jama’a suke bukatar wasu kalamai na tausayawa sai kuma ga wancan magana ta shugaba Buhari, don Allah me hakan ke nufi?

Babu shakka a wannan gabar, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’I ya nuna cewa ya san abinda yake fiye da shugaban kasa, domin maganar da ya yi a wannan waje lokacin da yakai ziyara, ita ce ya kamata ace shugaba kasa ya je har wajan ya yi ta, ba wai wani mutun ya koma daga Abuja yana magana a madaddinsa ba, wannan ba daidai bane.

“Muna bako hakuri na rashin gazawarmu wajan kareku daga farmakin ‘yan ta’ada da masu garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa, zamu yi duk yadda zamu yi domin ganin an kawo karshen wannan lamari” inji gwamnan Kaduna.

Baban abinda wannan gwamnati ta shugaban Buhari ta tsana shi ne, ace ta kasa ko ta gaza wajan kare rayuwakan jama’a tana matukar yaki da irin wannan kalamai, musmaman idan wani wanda ake ganin ba acikin gwamnati yake ba, da zaran ya yi su, to abinda zai biyo baya ba mai dadi ba ne.

Saboda haka ‘yan kasa suna da hakki a wajan wannan gwamnati da ‘ya bani na iya suka kewaye, ba sa son a fadi gaskiya, basa bukatar kowa a kusa da su, sun sakarwa sojoji kasar alhali ‘yar manuniya ta nuna cewa ba za su iya wannan aiki ba, taki yarda cewa ta kasa.

Idan har za a cigaba da tafiya a haka kamar yadda na sha fada abaya gaskiyar magana ba mu san inda za a tsaya ba, kafin wa’adin wannan gwamnati ya zo sai wanda Allah yasa yana da sauran numfashi zai kai labari.

Kai ka ce wannan gwamnati da sunan shekar da jinanan al’umma aka yi yakin neman zabanta, kuma ko a jikinta, abinda kaiwa suka kwarai shi ne, da zaran wani abu ya faru sai ka ji sun ce, muna gab da kawo karshen ‘yan Boko Haram, wannan magana tuni ta fita daga ran ‘yan Najeriya.

Kamar yadda na fada, kuma yanzu ma zan kara fada, duk wadannan abubuwan da suke faruwa game da sha’anin tsaro, ya nuna karara wannan gwamnati ta kasa, duniya fa na kallon haka, kuma tarihi yana nan a rubuce, kuma hakkin wadanda suka yi wannan zabe yana nan ba su yafe ba, suna rokon Allah ya bi ma su kadi.

Ba wai akan maganar matsalar tsaro ba, a kowane irin lamari ‘yan Najeriya na bukatar magana mai dadi wanda zata sanyaya halin da suke ciki, ba su bukatar irin wadancan maganganu na ku, ma su kama da rainin wayau.

Na tabbata, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana gab da fara yin nadamar irin yaudarar da ya yi wa ‘yan Najeriya musamman akan matsalar tsaro wanda suke bukatar a shawo kanta fiye da komi a wannan lokaci, ba mu san da wadannan irin kalmomi shugaba Buhari zai yi amfani ba wajan neman gafarar ‘yan Najeriya domin dole sai an kai ga haka.

Muna kara tunawa wannan gwamnati game da matsalar tsaro wanda kullin sai rayuka sun salwanta kuma an kasa yin maganinta, gashi Allah kadai yasan irin dukiyar ‘yan kasa da ta I layar zana da sunan tsaro. Allah dai yana gani kuma duniya ma tana kallonku.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: