Connect with us

LABARAI

Ra’ayoyin Kanawa: Yi Wa Sarkin Kano Sunusi II Murabus

Published

on

Kano ta Dabo Ci Gari, jalla babbar Hausa, yaro ko da me ka zo an fi ka!!! Wadannan ne irin fitattun kirarin da ake yi wa Birnin Kano mafiya shahara a tarihi, saboda yanayin yadda komai na Kano ya ke shan bamban da na sauran a Arewacin Nijeriya. Hakan ya sanya batun siyasar Kano, Gwamnatin Kano, Kasuwancin Kano, Noman Kano ko Masarautar Kano su ka mamaye su kuma shahara a ko’ina matukar wata badakala ko jumurda sun taso a kansu.

Ranar Litinin daidai da 9 ga Maris, 2020, rana ce mai dimbin tarihi ga al`ummar Najeriya, Afrika da ma duniya bakidaya da kuma musamman ga Kanawan Dabo, domin ita ce ranar da wata sarkakiya tsakanin Gwamnatin Jihar ta Kano da Masarautar Kanon ta kai matukar gaya.

A wannan rana ne gwamnan ta tabbatar da an yi wa Mai Martaba Malam Sarkin Kano Muhammad Sunusi II murabus daga karagar Sarkin Kano a wani jawabi, wanda Sakataran Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya karanta kai tsaye ga duniya a Gidan Gwamnatin Kano.

Mai Martaba Murabus ya kwashe kwana 1,869, wato shekara biyar da wata uku kenan, ya na mulkin Masarautar Kano bayan da ya dare karagar a ranar 10 ga Yuni, 2014, inda a lokacin da a ka nada shi an samu sosuwar zuciya fadin jihar sakamakon rashin nada daya daga cikin ’ya’yan sarkin da ya gada, wato Mai Martaba Marigayi Alhaji Ado Bayero.

To, amma a yanzu ma da a ka yi ma sa murabus, Malam Sanusi II ya bar karagar mulkin ne zukatan al’ummar Kanawa a cikin wani yanayi na sosuwa, saboda yanayin yadda siyasa ta yi matukar dabaibaye murabus din nasa.

Kan wannan lamari ne Wakilin LEADERSHIP A YAU ya zagaya, domin jin ra`ayoyin mutanen Kano da kewaye har ma da wajen birnin daga bakin Kanawa, inda wasu su ka yadda a bayyana sunansu da abinda su ka fada, wasu kuma su ka umarci cewa Wakilinmu da ya sakaya sunayensu.

 

Auwal Ali Ibrahim, matashi dan shekara sama da 30, ya ce, wannan kalma sabuwa ce a gurinsa, domin bai taba jin an ce an cire Sarkin Kano ba sai yau, amma a cewarsa, da ma komai na iya faruwa idan a ka yi yi laakari da yadda Sarkin Kano Muhammad Sunusi II ya nuna goyan bayansa ga wata jamiyya da ba ta gwamnati ba a zaben 2019.

“Shi kuwa Dan siyasa idan ka nuna ba ka kaunar sa, balle kuma kujera irin ta Sarkin Kano, komai na iya faruwa,” a ta bakin Auwalu mazaunin Kofar Nassarawa kuma masanin Shari`a.

“Shawarata” a cewar Auwalu, “shi ne Sarki ya yi ya kokari ya gane cewa, darajarsa da basirar da Allah ya yi ma sa ta girmi Kano, domin ya na daya daga cikin mutane 100 masu ingantaccen tarihi da tasiri a duniya kuma ya na cikin mutane 17 masu ilimi da za su iya bada gudunmawa da za ta iya farfado da tattalin arzikin duniya da iliminsu na Tattalin Arziki.”

 

Wani bawan Allah mai suna Malam Tahir Jafar, mutumin Kano, wanda su ka yi waya da wakilinmu, inda ya ce, yanzu haka ya na Gombe, ra`ayinsa shi ne Sarkin Kano Muhammad Sunusi II ba ya taka-tsantsan da bakinsa. Don haka komai na iya faruwa a mulkinsa.

 

Hajiya Maryam Sani Yakasai, wata matar aure, ta ce, “cire sarki ko barinsa bai dame mu ba; halin da mu ke ciki shi ne mu ke rokon Allah ya kawo wa al`umma sauki ta lafiya da wadata.”

 

Shi kuwa Abdullahi Yunusa, ya ce, “ba damuwa da abin da gwamnati ta yi, amma inda Goje ya je, can Kaura zai je komai dadewa. Mu dai mu na tare da Sarkin Kano 100 bisa 100, kuma idan an ce an cire Sarki, don shiga siyasa, magabatansa ma sun nuna wanda su ke so a siyasa, kuma har sarauta an ba wa gwamnan siyasa a Kano, inda har wanda Sarkin Kano Ado Bayero ya baiwa ya ce sarautar da ya bayar ta Sardauna har ta fi ta ’Yan Sarki. Wannan ba siyasa ba ce? Kuma ya nuna goyan bayansa ga dan takarar gwamna na wannan lokacin.”

 

Shi kuwa wani bawan Allah mai suna Umaru Dattijo, dan kimanin shekaru 75, ya ce, “mu dai cire sarki ba mu ji dadi ba, amma Allah ya kawo wanda ya fi shi alkairi kuma wannan ba bakon abu ba ne, domin kakansa Muhammadu Sunusi I da ya samu matsala da Sardaunan Sokoto murabus ya yi ya koma Azare bayan ya shekara 10 ya na mulkin Kano Sarki.”

 

Wani matashi mai karatu a jami`a mai suna Rabiu, wanda a ke yi ma sa lakabi da Kwankwaso, ya ce, bai ji dadin cire babansu ba, domin Sarkin Kano babansu ne.

 

Haka shi ma wani makusanci ga fadar Sarkin Kano, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “siyasa ce ta janyo wa sarki a ka tsige shi, amma dai mu na rokon Allah ya kawo wanda ya fi shi kuma Allah ya kawo zaman lafiya a Kano da kasa bakidaya.

 

Haka shi ma wani malamin makaranta da ke Karamar Hukumar Kumbotso, ya ce, “da Gwamna Ganduje bai cire Sarki ba, da na ga laifin Gwamnan Kano, domin gaskiya Muhammadu Sunusi II ya yi sakaci da girmama aladun Kano, musamman lokacin da ya tura ’yarsa ta wakilce shi a wani taro da dai wasu abu da su ke da alaka da addini da alada na Kano. Ba haka ya kamata a samu Sarkin Kano ba.”

 

Haka dai mutane da dama, wadanda wakilin LEADERSHIP A YAU ya zanta da su kan wannan abu na cire Sarki Kano su ka bayyana ra’ayinsu, yayin da wasu na goyan bayan Gwamnatin Kano wasu kuma akasin haka kan tsige Sarkin Kano na 14 a Daular Fulani.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: