Connect with us

MAKALAR YAU

Tsige Sarkin Kano: Laifin Wa?

Published

on

Tsige Sarkin Kano: Laifin Wa?

 

A matsayina na dan jihar Kano kuma marubuci, na yi rubuce-rubuce da yawa game da rikicin Ganduje da Sunusi Lamido a shafukan kafofin sadarwa da shafina na jaridar Leasdership. Rubutu na karshe a jarida game da rikicin shine wanda na yi wa lakabi da “Sarki Sanusi: Gaba Kura Baya Sayaki” inda na yi kokarin jan hankali mai martaba Sarki ya jefar da kwallon mangwaro domin ya huta da kuda ta hanyar yin murabus cikin mutunci. Mutane daban-daban sun bada irin wannan shawara, amma kasancewar kaddara ta riga fata, Sarki bai ji wannan kiran ba har zuwa lokacin da tarihi ya maimaita kansa yayin da gwamnatin Kano ta tsige shi.

Babban abinda ya fi ba ni haushi game da wannan tsigewa shine jefa Kanawa cikin wannan rigima inda su ka rabu gida biyu, wasu na goyon bayan Sarki wasu kuma na goyon bayan Ganduje. Sannan ba gaira ba dalili rikicin ya jawo gurguncewar tsarin masarautar Kano. Masaurautar Kano ta kasance daya daga cikin mafi tsufa a Afirka domin a tsawon shekaru 1000 ta ga sarakuna 57 zuwa yanzu. Kano ta yi rawar gani tun zamanin baya har zuwa zamanin cinikayyar ratsa Hamada (Tran-Sahara) da lokacin zuwan turawa har bayan tafiyarsu. Masauratar ta zama wani ginshiki na dunkule kanawa a matsayin wata al’umma wadda ta baiwa duniya gudunmuwa. Sarakunan Kano a tsawon tarihi sun kasance wadanda a ke girmamawa a harkar sarautar gargajiya a kasar nan. Wannan rikici da kuma tsige Sarki Sanusi hakika ya kawo karshen ragowar kima da iko da wannan masarauta ta yi daruruwan shekaru a kai.

A ganina, dalilai guda hudu su ka taka rawar gani wajen taimakawa yadda wannan rigima ta gama rusa masauratar Kano. Dalilin farko shine Shugaba Buhari, domin shi kadai ne a yau, da ya so, zai iya kashe wannan wutar rikici tun kafin ta kazance amma sai ya yi kunnen-uwar-shegu da matsalar. A zato na, duk irin matsalar da ke tsakanin Shugaba Buhari da Sarki, ya ci ace sarkin ya ci albarkar Kanawa saboda irin soyayya da biyayya da kanawa su ka ba Buhari fiye da yan jiharsa. Amma sai ya gwammace ya ki shiga tsakani tare da bada gurguwar hujja na rashin yin hakan. Hakika yadda Ganduje ya dauki Buhari tun farko, a matsayin hanya daya wadda zai kai ga cika burikansa, dalilin da ya kai shi jan daga da fito-na-fito da Kwankwaso, idan da Buhari ya ce masa ya hakura da rigimar na tabbatar zai tsaya nan take. Babu wani uban kirki da zai ga yayansa su na fada amma ya shuri takalmansa ya wuce ba tare da rabasa su ba. A tarbiya da al’adarmu wane irin uba ne zai aikata haka?

Abu na biyu da ya assasa rikicin shine halin rashin yafiya da Ganduje ya nuna tare da tsawaita rigimar yadda sai da ta mamaye duk al’umma sannan ya yi hukuncin da ya kamata a ce tun dawowar sa mulki karo na biyu ya dauka ko don ya ceci kanawa da fadawa cikin rikicin. Koda yakedai Sarki shi ya fara tsokana domin a wajen taron manyan arewa ya tashi ya soki gwamna Ganduje saboda shirinsa na yin titin jirgin kasa na wasu yan kilomitoci a birnin Kano wanda zai lakume dala biliyan $1.2. Sai dai kuma wannan suka ta taimaki kanawa domin dalilinta a kai watsi da shirin aikin wanda bas hi al’ummar ke bukata ba a wannan lokaci. Tun daga wannan lokaci Ganduje ya kullace Sanusi kuma ya daura damarar yaki wanda sai a wannan lokaci ya sami nasarar murkushe sarkin gaba daya. Duk wanda ya san Ganduje da kuma ganin yadda Buhari ya yi kememe ya ki saka baki cikin rikicin ya san cewa tsige Sanusi lokaci kawai ya ke jira.

Idan giwaye biyu na fada, an ce ciyawa ce ta fi shan wahala, to a wannan rikicin, gidan Dabo ne su ka kasance ciyawa domin saboda son rai na biyan bukatar kai, ya kai ga kacaccala gidan tare da haifar da gaba wadda Allah kadai ya san ina za ta tsaya. A fakaice da hannunsu sun rusa masauratarsu da kansu kuma har abada ba za ta sake dawo da kimar da a ka santa da ita ba har abada. Hakika Sarki Sunusi shi zai kasance sarki na karshe wanda ya sami mubaya’ar al’ummarsa kuma ya yi mulki mai cikakken iko karkashin masarautar. Duk wanda zai gaji wannan karaga ba zai taba samun irin kimar da Sunusi ya samu ba. Don haka gidan dabo su su ka fi kowa asara cikin wannan dambarwa.

Dalili na karshe kuwa shine shi kansa Sunusi Lamido ya bada gagarumar gudunmuwa wajen wannan dambarwa. Domin tun ya na dan yaro ya taso da burin gadon wannan kujera ta kakansa sakamakon tsige kakansa da irin wahalar da iyalinsu su ka fuskanta a wancan lokaci, kamar yadda ya gaya min a wata doguwar hira da muka taba yi da shi a gidansa na Gandu tun ya na banki. Irin ni’ima da Allah ya yi wa Sunusi Lamido, ka na iya cewa duk Kano ba wanda ya sami irin ni’imominsa, domin ya kasance gogaggen masani a fannukan boko da addini, sannan ya kai makura a harkar aikin banki inda ya zama gwamnan babban bankin Najeriya. Dadin dadawa ya sami shiga cikin jerin mutane 100 a duniya da su ka fi tasiri, matsayin da ba wani dan Kano da ya taba samu. Sannan mafi mahimmanci shine cika masa burinsa mafi girma a duniya na darewa karagar mulkin Kano, kuma a daidai lokacin da ya shiga tsaka-mai-wuya a lokacin da Jonathan ya dakatar da shi a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya.

Maimakon daga hawa mulkinsa ya maida hankalinsa wajen ganin ya fito da tsare-tsare wadanda za su shafi talakawa kai tsaye sai ya bige da soke-soke na mutane da al’amura ba tare da la’akari da muhalli ko lokaci ba, duk da cewa yawancin zantukansa tsagwaron gaskiya ce. Amma ko Allah cewa ya yi a yi wa’azi da hikima. Hikima a wa’azi (fadar gaskiya) shine ka fadi gaskiya ta hanyoyin da za ta yi amfani. A lokacin da rikicinsu da Ganduje ya rincabe, cikin wani rubutu da na yi, na ba shi shawara kamar haka “Tarihi na neman maimaita kansa, domin shekaru hamsin da su ka gabata irin wannan rigima ita ta faru da kakansa Sunusi na 1 da Sardauna. Sardauna bai wuce gona-da-iri yadda Ganduje ya cusa al’umma cikin lamarin ba, tare da raunata masarauta da kirkirrar dokoki. Duk da cewa shi ma Sardauna ya yi amfani da damar da ya ke da ita a gwamnatance, amma iya kan sarkin ya tsaya inda ya tilasta shi yin murabus. Shi kuma sarki Sunusi na daya bai nace wajen rike kujerarsa ba, domin ya na fahimtar cewa an shirya sauke ko tahalin kaka sai ya gwammace ya yi murabus. Kuma irin kima da biyayya da ya samu ta al’umma har karshen rayuwarsa, ko Sardauna bai samu ba”

Idan ka dubi Sunusi Lamido da irin abubuwan da ya yi a baya zaka iya cewa siyasa ce ta fi dacewa da iliminsa da kwarewarsa kuma na taba rubutawa cewa idan da nine shi wallahi ba zan zauna yan siyasa na tsangwama ta ba,nan take sai inyi murabus in shiga siyasar in yi takarar gwamna, kuma zai iya ci ya dawo ya gyara rusa masauratarsa da aka yi amfani da gwamnati a ka tabbatar. Kai hatta takarar shugaban kasa zai iya yi. Amma son kujerar ya hana shi ganin wannan rami da ya fada a yanzu wanda zai iya gurgunta duk wata dama da zai iya samu a siyasance nan gaba.

A karshe dai Sarkin ya rasa kujerar tasa ta hanyar tsigewa amma ba shi ka dai ne yayi asara cikin wannan dambarwa ba, domin shi kansa Buhari ya yi gagarumar asarar kimarsa a idon kanawa da goyon bayansu (koda yake alamu sun nuna cewa ba abinda ya dame shi da hakan). Shi kuma Ganduje wannan halayya da ya ke ta yi,  sannu a hankali za ta juyo kansa nan da shekaru uku domin shi alhaki kwuikwuyo ne (faya-fayen bidiyo na nan a ajiye). Masauratar Kano ta yi manyan asarori, domin ta rasa karfin ikon da take das hi kafin wannan rikici, sannan ta rasa jarumin sarki mai ilimi wanda asara ce wadda ba zata taba maye gurbinta ba, baya ga gaba da suka bari ta mamaye gidan Dabo a yanzu. Ni kuma da sauran kanawa mun yi babbar asara, ba ta sarki kawai ba, sai ta irin rashin hadin kai da rarrabuwa da ya kunno mana sakamakon wannan dambarwa, baya ga rusa mana masarautar da muke alfahari da ita tare da tabbatar mana dacewa a yanzu, ba a kano kadai ba, a duk fadin arewa mun rasa dattawa irin na da wadanda ke shiga tsakani domin kawo maslaha a duk wani rikici day a kunno kai domin kwanciyar hankali tsakaninmu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: