Connect with us

NAZARI

Nau’i Da Matsalolin Al’adar Mata

Published

on

A makon jiya mun fara da bayyana ma’anar al’adar har muka tabo wasu abubuwa adadin kwanakinsa da kalarsa, mun tsaya akan kwanakin daukewar al’ada. To yau za mu dora insha Allah.

Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama shi ne zuwansa na farko sannan ya tabbata cewa jinin al’ada ne to ta sani ta balaga, dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau kanta, idan ta yi salatin Annabi za’a rubuta mata lada idan kuma ta bari samari suna jagwalgwalata ita za’a rubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai ta yi aure sannan za’a fara yi mata rubutu, kenan har azumi sai ta rama wanda ta sha.

Tabbatuwar Jinin Al’ada, Shifa abinda ya shafi jinin al’ada al’amari da Allah Madaukain Sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur’ani mai girma, Allah yana cewa: ‘’Kuma suna tambayarka dangane da al’ada, Kace: Shi jinin cutane, ku ni sanci (saduwa da) mata a lokacin al’ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka (suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba kuma yana son masu tsarkaka’’. Bakara, aya ta: 222.

Haka kuma ma’aikin Allah–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce, (Wannan) Wani abune da Allah ya dorawa mata ‘ya’yan Adam’’.

Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane ai sanadiyyar da yasa mata suke al’ada shi ne wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa’u ta ci a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala’ika ne ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya amayar da abin shi yasa maza basa yi. Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur’ani sun tabbatar da Annabi Adam ya ci itaciyar.

Shifa jinin al’ada kada amanta jinni ne da yake fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu, Allah madaukakin Sarki ya haliccishi domin ya zama abin ci ga yaro a lokacin da yake cikin mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da karfinta ya ragu sosai, sa Allah ya sanya shi ya zama abincinsa, shi yasa da kyar kaga mace tana da juna biyu (ciki) kuma tana al’ada.

Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar da shi nono jaririn yana sha amatsayin abinci, shi yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa kuma suna al’ada. Idan ya zamana mace bata da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya kasance ba inda zai je to shi ne sai ya taru a mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko bakwai, ya kan karu ko ya ragu a kan hakan –kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.

Karkasuwar Mata: Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al’ada, kashi na farko, itace wacce ta fara, kashi na biyu kuma; wacce ta saba, sannan sai kashi na uku; mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka.

1.Wacce Ta Fara, Ita wacce ta fara al’ada ya zama yinta na yanzu shi ne ganin al’adarta na farko a rayuwarta, to abinda dake kanta zata zuba idone ta ga kwanaki nawa ya dauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-biyarba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al’adaba, kenan mafi yawan kwanakin da zata saurara sune kwanaki shabiyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama (Isthala) cuta sai a nemi magani, anan nake cewa iyaye su kara sa ido akan ‘ya’yayansu mata su dungu tuntubarsu suna fahimtar da su tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko makamantan haka, wata babbar macece amma bata san menene jinin al’adaba ita dai kawai tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganinshi.

2.Wacce Ta Saba, Abinda ake nufi da wacce ta saba itace wacce ta gabatar da al’ada sau uku a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al’adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai muce sunanta wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki sanannu. Amma idan ta yi al’adar karo na farko kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar karo na uku kwanaki shida, to ba za’a kira wannan wacce ta saba
ba, domin ba ta da tsayayyun kwanaki.

Ita wacce ta saba wato wacce take da sanannun kwanakin al’ada to wadannan kwanakin sune kwanakin al’adarta, idan kwanakin suka cika al’adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada, amma idan kwanakin suka cika al’adar kuma bata daukeba sai ta kara kwanaki uku, haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki shabiyar su cika, misali idan al’adarta kwanaki biyarne sai kuma jinin bai daukeba a kwanaki biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan takwasdin sun zama shadaya idan bai daukeba sai ta kara uku sun zama sha-hudu idan bai daukeba sai ta kara kwana daya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al’ada, ko ya dauke ko bai daukeba domin kwanakin al’ada makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma sun cika, abinda ya ci gaba da zuwa ba sunan shi jinin al’ada sunanshi jinin cuta (Istihala) sai a nemi magani. Aduk kan wadancan kwanaki da aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na saurare sai ya dauke a kwana na daya cinkin hukun shikenen sai ta yi wankan tsarki.

Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al’ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: