Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ba Yanzu Na Fara Aikina A Harkar Lafiya Ba – Kansila

Published

on

Gudunmawar da zababbun masu rike da matsayi irin na siyasa za su baiwa al’ummar da suke Shugabanta, na da matukar yawa amma ilmi da lafiya na sahun gaba, wannan ce tasa wakilinmu ya gana da Kansilan lafiya na Karamar Hukumar nassarawa Hon. Harazimi Shu’aibu, inda ya bayyana irin gudunmawar da ya kaiwa Mazabarsa tin bayan hawansa wannan mukami na farko a matsayin Kansila karo na biyu.

Haka nan, ya kara da cewa tun bayan hawansa na farko yake bayar da gudunmawa a wannan Karamar Hukuma, domin wannan shi ne zabarsa da aka yi a karo na biyu kenan a Mazabarsa ta Kawaji. Ya ce, ba komai ne ya ja haka ba sai irin gudunmawar da ya bayar, sai ga shi yanzu Allah Ya kai shi ga matsayin Kansilan lafiya a wannan Karamar Hukuma ta Nassarawa.
“Wasu daga cikin irin ayyukan da muka gabatar na lafiya a wannan Karamar Hukuma su ne, gina Asibiti kamar guda shida, ni kaina a Mazabata an gina Asibiti mai cin kamar mutum hamsin. Har ma Dagacinmu na Unguwar Kawaji ya ce a baya sun dade suna meman irin wannan dama, amma ba ta zo ba sai a wannan lokaci.” Hon. bai tsaya a nan ba ya cigaba da bayyana kokarin Ciyaman din wannan Karamar Hukuma, Hon. Lamin Sani na mayar da wannan Asibiti na kwanciya.
Haka zalika, a cewar tasa akwai Sikainin da muka raba a duk Asibitocinmu guda biyar na wannan yanki, shi ma wannan abin godiya ne ga Allah, sannan idan muka komo bangaren magunguna shi ma Algon ba a bar shi a baya ba wajen raba su a duk fadin Asibitocinmu, kamar na haihuwa kuma kyauta ne.
Sannan bayan zuwanmu, akwai masu cutar Hawan Jini ko Maleriya wadanda su ma mun ba su kyauta sama da mutum dubu biyar, kuma dukkanin Asibitocinmu akwai gyada da ake bawa yara masu cutar yunwa, ita ma mun kawo ta mun raba kyauta, duk Asibitinmu na Karamar Hukumar Nassarawa mun wadata da wannan gyada saboda yara masu cutar yunwa.
Har ila yau, akwai abubuwan da Shugaban Karamar Hukumar ta Nassarawa yake yi da daman gaske, domin kuwa yana yin koyi ne da mai girama Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje musamman wajen gudanar da aikace-aikace na alhairi wadanda za su taimakawa rayuwar al’umma kai tsaye.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: