Connect with us

MAKALAR YAU

Hayaniya ‘Yar Facebook!

Published

on

facebook

Idan ba ka da wadata irin ta hakuri, ka rufa wa kanka asiri wurin takaita irin nau’in mutanen da za ka yi mu’amala da su a sahar sada zumunta ta ‘Facebook’.
Zai yiwu, duk da ba ni da tabbaci. Daga cikin dalilan da suka sa hukumar gudanarwar Facebook ta ke ta kokaren lalubo hanyoyin samar da ‘yanci ga masu mu’amala da kafar, shi ne don a baka ikon yin tankade da rairaya daidai da dandanonka da son ranka.
A fannin ilimin kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar dan adam, mun tafi kan cewa, an halicci mutane da bambancin gaske a tsakaninsu, wani dogo ne baki; wani kuma gajere ne fari. Wani na da dakwalen idanu, da manyan kunnuwa. Wani sai ka ga an yi shi da idanu ‘yan mitsi-mitsi kamar dan Chana. Wannan iko ne na Allah mai halitta. Saboda ba ka da zabin yadda ka ke so a halitto ka.
Bayan an yi maka zubi ta mutum, ba ya yiwuwa ka cika kuma ka amsa sunan mutum har sai ka gina ‘DABI’A’. Ita dabi’a (duk da akwai takaddama mai karfi kanta) kaso mafi tsoka daga gareta koyonsu ake yi. Dabi’a ita ce ke samar da mutum. Ita ke tasirantuwa a zuciyarsa, ta tasirantu a ganinsa, ta tasorantu a jinsa, sannan ta tasirantu a tunaninsa da fahimtarsa.
Idan kana so, da zaran ka hadu da mutum za ka iya karantar wanne iri ne shi, wannan kuwa ta hanyar nazarin dabi’arsa. Saboda ita ke juya komi na rayuwarmu. Idan mutum dolo ne, kana ganinsa za ka fahimci cewa ya tasirantu da rayuwa cikin dolaye. Idan maketaci ne, ya koyi keta daga gida, ko wurin abokai, ko a makaranta, ko a unguwa. Idan ka ga mai natsuwa da kamun kai – ya koya ne walau a gida, ko a makaranta, ko wurin abokai.
Mutane da yawa za su so su kasance cikin jerin masu natsuwa da kamun kai. Ba nan gizo ke sakar ba. Iya kiyayewa da kare kamun kai ne abu mai wahala. Abu kadan na iya tunzura ka ka rushe kamun kan da ake kallonka da shi. Duk natsuwarka, kana iya aikata abu guda ko ka furta wata kalma da za ta sauke ka daga wannan matsayin a idon jama’a.
Akwai irin wadannan misalai masu tarin yawa, wadanda ke nuni da yadda za ka ga mutum mai natsuwa da kamun kai, amma ya gaza kiyaye kubecewarsu daga gare shi.
A hayaniya ‘yar facebook, za ka taras da mutane mabambanta, kowa da irin dabi’arsa. Wani kwararre ne a harkar gardama, ga naci da kafiridin sai an san da zamansa. A komi yana da ra’ayi, sannan duk wanda ya bambanta da shi a mahanga, an yi ta jinsu kenan.
Babbar matsalar hayaniya ‘yar Facebook shi ne mutane sun dauka cewa, gardama da soke-soke suna iya sauya tunani, mahanga, ko fikirar da suka cakudu da dabi’a wurin ginuwa. Shi ya sa a farkon rubutun nan na dan yi sharar fage dangane da dabi’a. Domin a ka’ida ta hankali shi ne, kafin ka hukunta mutum, yana da kyau ka san dan wani abu dangane da dabi’arsa. Idan mutum ya ce, ga matsayarsa ko fahimtarsa, kai kuma kana da wata matsayar ta daban. Mene ne abin zagi, da hauragiya? Ai kamar yadda hancinku da zubin kunnuwanku ba iri guda ba ne, haka dabi’arku.
A irin hayaniya ta Facebook ne za ka ga tsagera mai tulin ilimi, shi burinsa kawai manya su karkace ya dare kan wuyansu ya yi ta tsalle yana diban albarka. Tarin karatu ba shi ke nufin kana da lasisin saitawa ko gina dabi’ar wanda kuka saba da shi.
A hayaniyar Facebook ne za ka ga mutum da tarin shekaru, sai ya rika fakewa da girma yana sa kansa a gurbin hedimastan kula da abin da wasu (musamman wadanda ya sani) suke aikatawa. Ya yi ta katsalandan, har ta kai an fara keta rigar shekarunsa.
Yana da kyau mu fahimci cewa, ‘DON SHIRU A KE TSORON GAWA’, a wasu lokutan mafi alheri garemu da mutuncinmu shi ne yin shiru. Idan a komi sai mun yi tsokaci ko mun saki baki, za mu rika haifarwa da kanmu kafofin da za a keta mu. Abu mafi sauki a hayaniyar Facebook shi ne ka yi magana kan wani lamari da ke faruwa, sai wani ya yi kwament da ‘Karya ne’. shi kuwa duk wanda aka cewa makaryaci, za a iya watso mishi kowacce irin baka.
Idan kana facebook, ka bude zuciyarka, ka kuma fadada hangenka. Domin wuri ne da ke cike da hayaniya da rashin hankali, Facebook kafa ce da ke dauke da masu tarin karatu amma ba natsuwa. Ga tulin Masanan da basu da saiti. Tsaf! Za a kifar da kai ta baibai. Idan kai mai yawan fushi ne, shi kenan an gamu! Don kullum ka yi ta kumbure-kumbure kenan, domin hayaniya ‘yar Facebook ba ta karewa. Kullum akwai maudu’i.
Mu hadu mako mai zuwa!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: