Connect with us

RAHOTANNI

Tarbiyyatil Islamiyya Ta Yi BIkin Saukar Karatun Alkur’ani Karo Na 14

Published

on

Madarasatul Tarbiyyatil Islamiyya Wallugatil Arabiyya dake Danraka Samaru a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna ta yi bukin saukar karatun Al’kur’ani karo na 14.

Wakilinmu ya samu halartar taron Kuma ya aiko mana da rahoton yadda bukin ya gudana kamar haka.
Bukin saukar an gudanar da shi ne a bubban dakin taro na I.A.R da ke harabar A.B.U Zariya.
Alhaji Dakta Lema Jibril Dan Iyan Katsina ne ya jagoranci taron baya ga sauran manyan baki.
Bayan bude taro da addu’a sai aka malam Hasan damar bayyana  makasudin taron wato bayar da shaida ga wadanda suka haddace Al’kur’ani da wadanda suka sauka Al’kur’ani da karrama wasu fitattun mutane da suke yiwa addini hidima ciki harda Malam Ya’u Lukoro da Shamsuddin Dawu.
Bayan kammala karatun dalubai masu sauka ne maza da mata  aka bayyanawa Jama’a tarihin makarantar kamar haka.
Ita makarantar an kafa ta ne tun shekarar 1981 da malami daya da dalubai 39 kuma a zauren wani bawan Allah ne mai suna Alhaji Halilu ne aka fara, Allah ya jikansa da gafara.
Cikin ikon Allah yanzu makarantar na da dalubai 3424 da azuzuwan 11.
Baya ga haka an bayyana cewa daga 1981 zuwa 2020 wannan makaranta ta yaye dalubai 575 da mahaddata Alkur’ani Mai girma guda 34 bangaren matan aure da suka sauka an samu guda 168.
Wannan makaranta bincike ya tabbatar da cewa tana da bangarori da dama da take gudanarwa kamar haka sashen yara da matan aure sai haddan Al’kur’ani Kuma suna da sashen magidanta da ‘yan jami’a.
Daga cikin nasarar da aka kawo da makarantar ta samu akwai bayar da tarbiyya ga matasa da zuwa gasar karatu daga karamar hukumar har zuwa jiha da Kasa baki daya.
Wasu nasarorin kuma sune tsaftace zukatan yara maza da mata da matan aure daga fadawa shaye-shaye,
Sai samar wa makarantar da ma wasu makarantun malaman Al’kur’ani wadanda ake cin gajiyayyu har zuwa yau,
ilimantar da yara masu tasowa littafin Allah tare da tajwidin sa, hada kan al’umma ba tare da nuna kabilancin yare ko launin fata ba, ingantacce tarbiyya al’umma ta hanyar Basu ilimin addini da na zamani domin akasarin malaman Islamiyya da ke Samaru da kewaye daga wannan makaranta aka yaye su, shiryawa da gudanar da wa’azin addinin musulunci a watan Ramadan da sauran watannin musulunci, samun nasarorin gasar karatun Al’kur’ani tun daga karamar hukumar har zuwa kasa baki daya, samun nasarar gina azuzuwan 6-11 tare da babban masallaci da taimako da a ke samu daga wasu bayin Allah.
Wasu matsalolin makarantar sun hada da bukatar goyon bayan iyaye wajen sanya ido ga abokan ‘ya ‘yansu domin rashin sanya Ido ga abokanan yara matsala ce babba wadda makaranta ke fuskanta, akwai bukatar iyaye su rinka binciken me ake koyawa yaransu a makaranta Kuma su rika biyan kudin makaranta a kan lokaci domin akasarin iyaye basa son biyan kudin makaranta Kuma idan an yi kira su taro ba sa halartar taron da sauran wasu matsalolin.
Kudirorin makarantar dai sun hada da siyan wani gida a Nan kusa da Islamiyya da Kuma bayyana cewa daga watan Afirilun 2020 kudin makarantar zai koma 500 a kowanne zangon karatu.
Sheikh Khidir Manufa ne ya yi nasiha ga mutanen da suke wajen taron a kan muhimmanci bayar da taimako ga addini ya ce a yi koyi da Sayyidina Abubakar da Usman da Umar wajen yi wa addini hidima.
Haka shi ma Sheikh Jamilu Albani Samaru kira ya yi ga dalubai da su dage wajen karatu da kaucewa girman kai.
Daga cikin bakin da suka samu zuwa akwai Mai girma hakimin Basawa Munir Jafaru sai Dakta Lemu Jibril Dan Iyan Katsina da Farfesa Ahmad Abdullah OON (Cigarin Nupe)
An yi taro lafiya kuma an tashi Lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: