Connect with us

WASANNI

Chelsea Ta Hakura Da Timo Werner Ta Koma Neman Dembele

Published

on

werner

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta hakura da zawarcin da take yiwa dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig, inda a yanzu ta mayar da hankalinta wajen zawarcin dan wasan Lyon, Moussa Dembele

Dembele, mai shekara 23 a duniya dai yana daya daga cikin ‘yan wasan gaba a gasar firimiya da tauraruwarsu take haskawa kuma kungiyoyin firimiya da suka hada da Manchester United da Chelsea ne suke zawarcinsa.

Kamar yadda rahotanni daga kasar Faransa suka bayyana Chelsea ta hakura da ci gaba da zawarcin dan wasa Timo Werner wanda kungiyar kwallon kafa ta Liberpool take zawarci kuma shima dan wasan yafi kaunar zuwa Liberpool din.

Tun a watan Janairu kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea yaso kungiyar ta sayo masa dan wasan gaba wanda zai zama kishiya ga Tommy Abraham wanda yake fama da ciwo sannan Olivier Giroud bashi da tabbacin zaman kungiyar duk da haka.

Sai dai a kwanakin baya kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United yaje har kasar Faransa yaga dan wasan kuma shima yana son sayan dan wasan gaba mai zura kwallo a raga wanda hakan yake nufin Chelsea za ta samu kalubale daga United.

Moussa Dembele dai, wanda ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Celtis ta kasar Scotland da Fulham ta Ingila ya zura kwallaye 16 cikin wasanni 27 daya buga a kungiyar kwallon kafa ta Lyon a kasar Faransa
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: