Connect with us

RAHOTANNI

Gombe Ta Dauki Matakan Shawo Kan Yajin Aikin Likitoci, Cewar Kwamishinan Lafiya

Published

on

Gwamnatin Jihar Gombe ta shaida cewar ta dauki matakan da su ka dace domin shawo kan matsalar yajin aikin da likitocin da su ke jihar suka tsunduma, gwamnatin tana mai nuna damuwarta kan shiga yajin aikin likitocin a daidai lokacin da cutar Koronabairus da zazzabin Lassa ke yaduwa a fadin duniya, sai ta bayar da tabbacin yin duk mai iyuwa domin shawo kan matsalolin.

Kwamishinan lafiya na jihar Gombe, Dakta Ahmad Muhammad Gana, shine ya shaida hakan a wani taron manema labaru da suka kira a shekaran jiya, yana mai karawa da cewa, gwamnatin jihar ta dauki kwararan matakan da suka dace domin tabbatar da shawo kan yajin aikin da kungiyar Likitoci a jihar suka tsunduma ‘Association of Resident Doctors (ARD)’ domin tabbatar da ci gaba da bayar da tasu gudunmawan kai kiwon lafiyan jama’a.

“Abin takaici da damuwa ne a ce kungiyar ta dauki matakin shiga yajin aiki a daidai lokacin da duniya take fuskantar bazaranar cutar numfashi mai hanzarin illa wato Koronabairus (COBID-19) da sauran cutuka masu yaduwa kamar su zazzabin Lassa. Wanda ma abin bunkata ne a ce, tsoffin ma’aikatan lafiya su kansu su bayar da tasu gudunmawar a irin wannan lokacin ba ma wai a samu wadanda suke kan aikin suna yajin aiki ba,” Inji Shi.

Ya kara da cewa, irin wannan yajin aikin ya so ya sha banban da tsarin koyarwar aikin likitanci da kuma kula da lafiyar jama’a domin barazanar da ake fuskanta ya zarce batun tsunduma yajin aiki.

Yana mai karawa da cewa abin lura ne ta irin kokarin da gwamnatin jihar take yi wa likitocin wanda ya ma ce yanzu haka suna cin gajiyar sabon tsarin albashi mafi karanci.

“Gwamnati mai ci ta dauki sashin kiwon lafiya a matsayin daya daga cikin muhimman bangarorin da ta sanya a gaba, duk kuwa da matsanancin yanayin tattalin arziki, gwamnati ta sanya makuden kudade ga sashin da suka hada da sake miliyan dari uku da hamshin (N350m) a yanzu haka domin yin kwaskwarima wa asibitin kwararru da ke jihar. Biyan naira miliyan dari hudu da shirin da uku (N423m) na kudin hadaka da kungiyoyin tallafi daban-daban a jihar dukka da suka shafi harkar lafiya.

“Sake naira miliyan (N605m) ga shirin N-SHIP domin tabbatar da jihar ta samu cin gajiyar shirin a fadin kananan hukumomin jihar guda 11 da zai tabbatar da samar da cibiyar kula da lafiya a kowace gunduma. Sake naira miliyan (N42m) domin shirin ko-ta-kwana na dakile barkewar cutuka da suka hada da zazzabin Lassa da Koronabairus a jihar. Sake naira miliyan (N160m) domin biyan kudin tallafi ga jami’an kiwon lafiya masu sa-kai domin tabbatar da samar da jami’an kiwon lafiyan jama’a a fadi jihar, da sauran muhimman kokarin da gwamnati mai ci take yi kan kiwon lafiyan jama’a kawo yanzu,” A cewar Kwamishinan.

Dakta Ahmad Muhammad Gana ya kuma shaida cewar bukatun Likitocin ba wai sune suka haifar ba, sun gada ne daga gwamnatin da ta gabace da suka zarce shekaru uku suna fama da bukatun nasu. Kodayake, ya ce gwamnati tana da cikakken masaniya kan matsalolin na likitocin sai ya ce tunin aka sanya komai kan mizani domin tabbatar da shawo kan matsalolin.

“A dan kankanin lokaci, gwamnati ta sake naira miliyan (N5.65m) ga gidajen jami’ai guda 13. Sauran kokarin da aka yi sun hada da samar da hukumar kula da asibitoci ta jihar da tsarin asusun tallafi ga kiwon lafiya ta ‘State Contributory Health Scheme’ dukka a cikin kokarin gwamnatin na shawo kan wasu matsalolin.

”A cewar Dakta Gana, tunin ma’aikatarsu ta lafiya ta kira ganawar gaggauwa domin tattauna muhimman batutuwan da za su kyautata sashin lafiya, inda ya ce akwai manyan daktoci da wasu jami’an kiwon lafiya da yajin aikin bai shafa ba, don haka suna ci gaba da aikin kula da lafiyar jama’an jihar.

Daga bisani ya roki jama’an jihar da su ci gaba da neman kulawa kan kiwon lafiyarsu a dukkanin asibitocin da suke fadin jihar yana mai basu tabbacin gwamnati na kan kokarin tabbatar da kyautata sashin a kowani lokaci, sai ya nemi su kwantar da hankulansu domin gwamnati na sane da komai domin shawo kan matsalolin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: