Connect with us

WASANNI

Kashi 35 Na ‘Yan Wasan Valencia Sun Kamu Da Coronavirus

Published

on

valencia

Kungiyar kwallon kafa ta Valencia dake kasar Sipaniya ta bayyana cewa kashi 35% cikin 100 na ‘yan wasa da ma’aikatan kungiyar sun kamu da cutar Coronabirus sakamakon yadda cutar take ci gaba da yaduwa a duniya.

Kungiyar kwallon kafa ta Balencia, wadda take buga gasar rukuni-rukuni ta kasar Sipaniya ta buga wasa da kungiyar Atlanta dake kasar Italiya a ranar 19 ga watan February dalilin daya sa ake ganin a wannan lokacin ne suka kamu da cutar saboda daman ‘yan kasar Italiya sunfi kamuwa da cutar musamman a nahiyar turai.

Bayan da aka ci gaba da samun alamu da tsoro a zukatan shugabanni da masu koyarwa da ‘yan wasan kungiyar ne sai aka bawa kowa umarni da yaje domin a gwada lafiyarsa kuma a haka ne aka gano halin da kungiyar take ciki.

A ranar Litinin ne kungiyar ta ce ‘yan wasan kungiyar da suka kamu da cutar tun farko suna ci gaba da murmurewa ya yin da ake ba su kulawar da ta dace kuma babu wata damuwa a tattare dasu sannan kuma kungiyar ta bayyana cewa tana daukar dukkan matakan kariya domin kula da wadanda basu dauka ba.

Dan wasan bayan kungiyar kuma dan kasar Argentina, Ezekuiel Garay ne dan wasa na farko a La Liga da ya bayar da sanarwar kamuwa da cutar a ranar Lahadin data gabata sai dai daga baya an sake gano wasu daga cikin ‘yan wasan cikin har da Elekuim Mangala.

Valencia tana mataki na bakwai akan teburin laligar bana kuma tayi rashin nasara a gasar kofin zakarun turai zagaye na 16 da kungiyar Atlanta ta doke ta daci 8-4 a gaba daya wasanni biyun sai dai tun a ranar Alhamis din data gabata ne aka dakatar da gasar ta La Liga bayan killace tawagar Real Madrid kuma kasar Spaniya ce kasa ta biyu da cutar ta fi kamari a Nahiyar Turai bayan Italiya kuma tana kokarin saka dokar-ta-baci ranar Litinin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: