Connect with us

WASANNI

Liverpool Ta Fi Kowacce Kungiya Tsada A Duniya – Rahoto

Published

on

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ce ta fi ko wacce tsada a kasuwar musayen ‘yan wasa tsakanin manyan Gasannin Turai biyar, kamar yadda binciken kungiyar CIES da ke bibiyar kwallon kafa ya bayyana.

Liverpool ta haura takwararta ta gasar firimiya, Manchester City da yawan kudin da suka kai yuro biliyan 1.4, wanda suka yi daidai da fam biliyan 1.27, yayin da Manchester City take da fam biliyan 1.24, kuma take matsayi na biyu a jerin.

Chelsea ce ta biyar a jadawalin, yayin da Manchester United da Tottenham ke cikin jerin kungiyoyi goman farko kamar yadda wannan hukumar ta fitar da alkaluman ta a wannan satin da muke ciki.

Da jumlar darajar kudi da suka kai fam miliyan 33.7 kungiyoyin Bundesliga su ne a karshen jadawalin duk da cewa akwai manyan kungiyoyi a kasar da suka hada da Bayern Munchen da Dortmund.

Liverpool da ke jan ragamar Gasar firimiya na bukatar cin wasa biyu ne kawai cikin wasanni taran da suka yi ragowa a gasar domin ta lashe ta, karo na farko kenan cikin shekara 30 sannan ta lashe Gasar Zakarun Turai a bara ta kuma kara da kofin Uefa Super Cup tare da kofin zakarun nahiyoyi duk a lokaci guda.

Mai koyarwa Frank Lampard ne ke matsayi na biyar a jadawalin, inda tawagarsa ta kai darajar kudi fam miliyan 917 sai dai CIES ta ce darajarta ta kara dagawa sakamakon barkewar annobar da ta shafi da yawa daga cikin matasan ‘yan kwallonta, da kuma hana mata damar sayen ‘yan wasa da Fifa ta yi.

CIES ta yi amfani da ma’aunai daban-daban wajen fitar da darajar kungiyoyin, wadanda suka hada da shekarun ‘yan kwallo da kokarinsu da tattalin arzikin kungiyar da dai sauransu kamar yadda sanarwar ta bayyana.Kylian Mbappe na Paris St-Germain mai shekara 21, shi ne ya fi ko wanne dan wasa daraja wanda ya haura fam miliyan 227 sai kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Dortmund, Erling Braut Haaland.

Jerin Kungiyoyin Da Sukafi Daraja

Liverpool England 1,405

Man City England 1,361

Barcelona Spain 1,170

Real Madrid Spain 1,100

Chelsea England 1,008

Man United England 1,007

Paris St-Germain France 979

Atletico Madrid Spain 836

Tottenham England 787

Jubentus Italy 783
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: