Connect with us

MAKALAR YAU

Majalisar Dattawan Nijeriya: Bawa Ba Ya Zama Da

Published

on

Ma’anar Majalisa baya wuce wani gungun mutane da aka zaba a jam’iyyun siyasa mabanbanta ko su ka ci da karfi ko a ka kwace, domin su zama wakilin jama’a a matakin gwamnatin tarayya, sannan akwai irin wannan majalisa a matakin kowace jiha kuma kamar aiki su irin daya ne.

Abin mamaki a Najeriya ba haka lamarin yake ba, domin kuwa idan aka duba ma’anar majalisun Najeriya lallai zai yi hannun riga da ainahin ma’anar da aka bata tun farko.

Sai dai abubuwan da ‘yan Najeriya suka yi tsammani game da wannan majalisa ta dattawan Najeriya shi su ke gani, duk da cewa shugabancin majalisar ya yi kokarin wajan ganin ya nuna cewa ba za su taba zama ‘yan amshin shata ba.

To, amma abubuwan da suke faruwa a wannan zaure, gara abinda ‘yan amshin shata suke yin na nishadantar da mutane, ba wai kunsa mu so bakin ciki ba kullin da sunan wakilici.

Sai a wannan lokacin ne aka kara gane dalilin da yasa gwamnatin shugaba Buhari da wasu makusantanshi suka dora karan tsana akan shugabancin majalisar da ya gabata duk da cewa ‘yan jam’iyya mai mulki ne suka jagorancin majalisar.

Idan muka yi waiwaye adon tafiya zamu ga cewa su wadannan majalisu ana yin su ko ana samar da su domin wakilicin jama’ar da suka zabe su dangane da bukatunsu da yau da kullin tare da kare hakkinsu akan duk wani abu da zai ta so.

Daman tuni masana harkokin siyasar Najeriya suke bada fassara daban-daban game da wannan majalisa ta tara, saboda yadda suka ga an fara nuna wadanda ake son su jagorancin shugabanta, ga alama ba su da banbanci da masu dumama kujera idan ta yi zafi su huce akan talaka.

Batun da ke tasowa yanzu daga wannan majalisa na kafa dokar da zata hana shigowa da kuma sayar da na’urar bada hasken wutar lantarki a Najeriya wato injin Janareto abu ne da ya kamata ace duniya ta yi wa wannan majalisa dariya da Allah wa dai akan abinda suke niyyar yi.

Ni na sani, kowa ya sani duk lokacin da aka ce za a dauki wani mataki ga ‘yan Najerya idan aka duba da kyau za a ga cewa, akwai wanda ake hari abin ya kai gare shi, wato shi ne talaka, domin sai kara tabbata take yi cewa a Najeriya doka tana hawa akan talaka ne kawai.

Idan kuwa haka ne, ya kamata mu kara yin karatun ta nutsu domin kalubalantar duk wani sha ci fadi da zai fito daga bakin wadannan mutane, kuma alamu na nuni da cewa wannan shugabancin majalisa ta dattawa ta tara, zai kasance mafi muni a tarihin siyasar Najeriya.

Abin takaici ne ga ‘yan Najeriya a nuna su Ahmad Lawan a matsayin shuwagabanin Majalisar Dattawan Najeriya, a daidai lokacin da ake neman mutane wadanda za su yi tsayin daka wajan ganin an fita daga halin kuncin rayuwa.

Amma da yake ba talakwa bane suka yin wannan zabe ba, sai ga shi an samar da wadanda rashin su ya fi amfani ga rayuwar talakan Najeriya, a maimakon samar da su, saboda ba abinda suka sani, sai kan su.

Duk wanda ka gani a wannan majalisa yana da dalilin zuwansa sabanin abinda aka zabeshi ya je ya yi, idan ma da kujerar halas yaje ke nan, amma wasu ba su da abinda ya suka sa gaba kamar neman duniyar su, domin gudun kadda su talauce nan gaba, ko kuma ana neman mukamin da ya fi wanda ake akan shi.

Doka dai a Najeriya ba sabon abu ne ba, sai dai duk lokacin da aka yi ta kamar yadda na fada, tana karewa ne akan talaka, idan muka duba baki daya, wake amfani da injin Janareto, za ka ga cewa kaso mafi tsoka wadanda ake kira manyan Najeriya ne.Idan haka ya zama gaskiya, to za mu ga cewa lallai talakan Najeriya yana amfani da Janarato ne saboda baya da zabin da ya wuce haka, idan kuwa yana da shi, lallai ba zai kalli wajan da ake yin maganar doka ba saboda ya san ba da shi ake ba.

Zan bada misali da lokacin marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, jami’an tsaro a wannan lokacin suna farautar masu sayar da man fetir da ake kira “Black Market” ko ‘yar cuwa-cuwa ko kuma ‘yan Bunburutu, wannan matsala kuwa ta taho ne daga burfishin gwamnatin sojoji.

A lokacin da Umaru Musa Ya zama shugaban kasa, bai sa dokar ta baci ba akan ‘yan black Market ba, sai ya bullo da wata hanyar wanda muka yi zato cewa wannan gwamnatin zata yi amfani da irin wannan hanyar, a wancan lokaci sai aka samar da wadataccen man fetir ko’ina a cikin Najeriya saboda haka ba tare da an takurawa ‘yan bunburutu ba, wannan dabi’a ta kwanta dama cikin ruwan sanyi.

Ko a wancan lokacin baban dalilin da yasa ake farautarsu, bai wuce yadda suke boye mai ba, daga baya kuma wuta ta rika kamawa a cikin gidajan jama’a inda kuma ake samun asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Saboda haka sai mu ka yi zato cewa ‘yan amshin shata, za su yi amfani da basira da ilimin da suke da shi da sanin inda aka dosa, su tabbatar da cewa wannan kasa ta Najeriya ta samu wadatacciyar wutar lantarki domin ta haka ne kawai duk mai janareto zai jingine shi gefe guda ya yi amfani da harsken wutar lantarki da aka samar daga gwamnati wanda ta fi sauki da karfi da kuma bada kariya.

A shekarar 2010 mun kai ziyara kasar Nijar inda muka ziyarci wasu daga cikin gidajan talabijin na kasar amma mallakar ‘yan kasuwa, duk inda muka je bana ganin injin janareto wanda ko da an samu matsalar wuta, wannan tasa sai da na yi tambaya cewa yanzu idan aka dauke wuta ya ke nan? Amsar da wani jami’in gidan talabiji din ya bani ita ce, kai da jin wannan magana an san daga Najeriya kake, ya ce ai mu nan ba a dauke wuta, saboda haka babu wani tanadi na injin samar da hasken wuta saboda ba mu tunanin dauke wutar lantarki.Wannan magana da ya yi ta yi matukar tasiri a rayuwata musamman a lokacin da nake rubutun abubuwan da na gani a jamhuriyar Nijar wanda daman shi ne zuwa na farko baban birnin Kasar.

Na ga yadda ‘yan Najeriya suka rika maida martani dangane da wannan batu na kafa dokar da zata hana shigowa da kuma sayar da Janareto a Najeriya, wani da yasan yadda abubuwa suke tafiya cewa ya yi, gaskiya Sanatocin Najeriya sun kai makura wajan wasa da hankailin ‘yan kasa. Ya ce a lokacin da zauran majalisar dattawa yake tattauna wannan batu, hasken wutar lantarkin Janareto ne suke amfani da shi a dai dai wannan lokacin.

Wannan ya yi dai dai da wani lokaci acan baya da aka aikeni biyan kudin wuta, na taras babu an dauke wuta, sai da aka tada Janareto sannan aka iya karbar kudin, aka biya domin suna amfani ne da na’ura mai kwakwalwa wanda kuma take amfani da hasken wutar lartarki. Wani abu sai Najeriya, idan Allah ya kai mu, sati mai zuwa zan cigaba da wannan rubutu, sannan zan kawo farkon wannan muhawara ta samar da dokar da zata hana shigowa da kuma sayar da Janareto, sai dai har gobe mu na cewa Majalisar Dattawan Najeriya Bawa Ba Ya Zama Da, ko me ya aikata…

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: