Connect with us

TATTALIN ARZIKI

CBN Ya Ware Wa ’Yan Fim Da Mawaka Naira Biliyan 22

Published

on

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ware wa masana’antar shirin fim da mawaka Naira biliyan 22, don cin moriyar bashi mai sauki.

Daraktan Sadarwa, Mista Isaac Okorafor, wanda ya yi jawabi a yayin taron tattaunawa na hadin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki a kan manufofin shekaru biyar na Babban Bankin Nijeriya (CBN) a karshen mako a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, ya ce, matakin ya kara karfi ga masana’antar kamar yadda ta dauki jagorancin Afirka a gaba, inda ya kara da cewa, matakin zai kuma lashi takobin yin fashin baki yayin da ya ke samar da dalilai na asali.

Ya ce, Babban Bankin na CBN ya kuma yanke shawarar tayar da masana’antar da ta kera. “A halin yanzu, Nollywood da Kannywood da masana’antar kade-kaden Nijeriya su ne manyan masana’antar nishadi a Afirka. Ba za mu bar masana’antar ta fadi ba. A shirye mu ke mu tara kudaden ‘yan fim da masu shirya fina-finai a masana’antar.

“Kuma kasancewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ta ke da masana’antar kere-kere, za mu tallafa wa mutane a wannan fannin ma.

“Mun yanke hukuncin cewa dole ne mu farfado da masana’antar, mun fara ne ta hanyar ba da tallafi ga manoman da su ka dasa auduga; Mu na bayar da kudin daukacin darajar, don duk wanda ya taka rawa, ciki har da masu amfani da sutura da masu yin suttura, don kada ta karye. “Mu na yin hakan ne saboda idan tattalin arzikin kasar ba ya aiki da kyau, CBN ba zai iya yin nasa aikin ba.

Misali; a duk tsarin kudi da farashin kayayyaki, hauhawar farashin kayayyaki ba za ta iya zama kwanciyar hankali ba idan farashin abinci bai tsaya ba, saboda abinci ya fi yawa, sama da kashi 50 na abin da mu ke kashewa a Nijeriya.

“Idan mutane ba su da abincin da za su ci, yawan amfanin kasa ba zai karu ba, idan mutane ba su da abinci da za su ci lafiyar al’umma ba za ta iya zama ba, hakika lafiyayyen mutum ne wanda zai iya kawo ci gaba, kuma ya kawo ci gaban tattalin arziki Kuma a cikin yanayin da ba za a samar da ayyukan yi ba zai zama babu walwala, ma’aikata marasa aikin yi za su zama masu saukin kayan aiki a cikin hannun wadanda suka shirya gujewa laifi, ” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: