Connect with us

Da dimi-diminsa

LEADERSHIP Ta Karrama Fintiri Na Adamawa A Matsayin Gwamnan Shekarar 2019

Published

on

A ci gaba da taron karrama gwarazan LEADERSHIP na shekarar 2019, kamfanin ya karrama gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin gwarzon gwamna. Inda kamfanin ya yi amfani da kwanaki 100 na gwamnan akan mulki wajen ba shi wannan kyauta.

Gwamnan da kansa ya fito ya karbi wannan kyauta a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, kuma shugaban wannan taro.

Inda ya jinjinawa LEADERSHIP bisa zabo shi da ba shi wannan kyauta. Ya kuma fara ne da godewa Allah ta’ala bisa wannan dama da ya ba shi ya kasance gwamnan jihar Adamawa. Inda ya sha alwashin ganin jihar ta zama gaba a bangaren ci gaba a yankin Afrika ma baki daya.

Taron dai na ci gaba da gudana a dakin taro na ICC a Abuja.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: