Connect with us

TATTAUNAWA

Sauke Sarki Sanusi: Akwai Dalilan Rashin Barkewar Rikici A Kano – Sani Brothers

Published

on

ALHAJI SANI YUNUSA SARINA, wanda a ka fi sani da ALHAJI SANI BROTHERS, shi ne tsohon shugaban kungiyar motocin sufuri na biyu a tarihin Najeriya kuma dan kasuwa, manomi, mai kimanin shekaru 70 a duniya, sannan mai bin diddigin al`amuran yau da kullum tare da yin mai fashin baki. Ya bayyana dalilai masu yawa da su ka sa ba a yi wata hayaniya ko tashin hankali ba a Kano bayan an sami sauyin sarki bisa sauke Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda ya gaji Marigayin Mai Martaba Sarkin Kano Ado Bayero a cikin wani yanayin siyasa mai rudarwa.

Tattaunwar ta kuma kunshi bayanai a matakin Kano da kasa bakidaya a matsayinsa na daya daga cikin Kano, Arewa da ma Najeriya bakidaya a wannan hirar tasa da manema labarai a birnin Kano; cikin har da Wakilin LEADERSHIP A YAU, KANO MUSTAPHA IBRAHIM, ranar Juma`ar da ta gabata. Ga dai yadda hirar ta kasance:

A lokacin da a ka samu sauyin sarauta a Jihar Kano mutane da dama, musamman wadanda su ke wajen Kano, sun yi tunanin za a samu wani hargitsi ko tashin hankali, amma a ka zauna lafiya a jihar. Me ka ke ganin ya jawo haka?To, gaskiya mutane, musamman wadanda su ke wajen Kano, sun jahilci wayewa da hangen nesa irin na Kanawan Dabo, domin Kanawa ba su manta ba cewa, a nan Kano a ka yi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, wanda shekararsa 51 ya na mulki, kuma an zauna sa shi lafiya, ba sa rigima da kowa kuma a zahiri daidansa ta fi rashin daidanshi yawa, duk da ya ke dan adam tara ya ke bai cika 10 ba. Allah ya gafarta ma sa, Amin.

Kuma Allah ya ba shi ‘ya’ya mata 33, Maza 30. To, ka ga 63 kenan. Da Allah ya karbi ransa, dukkaninsu babu wanda a ka zaba a ka bai wa Sarkin Kano a cikinsu tun da sun nema an hana su, sai a ka nemo jikan sarki a ka ba shi sarautar su na kallo su ka hakura ba su ce komai ba. Duk mutanen Kano su na sane da wannan, amma dai su ka hakura tun da babu yadda za su su yi, duk da soyayya da zaman lafiyarsu da Sarkin Kano Marigayi Mai Martaba Alhaji Ado Bayero a ka yi wa ’ya’yansa haka a Kano.Baya ga wannan; duk da jimami da jin zafin rasuwar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Kanawa su ke jimami su ke ji har yanzu, amma a wannan lokacin Gwamnatin Kano ta wannan lokacin ko hutun minti 15 ba ta bayar ba, haka a ka wuce, duk da dadewarsa a kan mulki da kuma yawan ’ya’yansa, to don kuma an samu sauyi an sauke sarkin da ya gaji Ado Bayero, an sa dansa, to wacce rigima za a yi a Kano? Babu wata rigima! Kan wa za a yi rigimar? Har waya an yi min a na tambaya ta ‘Kano lafiya?’ na ke cewa ‘Kano lafiya lau kuma mu sai addu`a da fatan alkhairi a wannan jihar da kasa da ma duniya bakidaya’.

To, ganin a yanzu Kano ta samu sabon sarki, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ko akwai wani sako ga mMai Martaba?Shi alkhairi ba a jinkirin fadarsa. Don haka abinda zan ce shi ne kowa ya san Marigayi Alhaji Ado Bayero mutum ne mai hakuri da juriya da kau da kai da cika alkawari a duk lokacin da ya dauka. Ko da a wajen taro ne ba ka taba jin an ce Marigayi Ado Bayero ya makara ba a wani taro ba, sannan kuma ba ka taba jin an ce Marigayi Sarkin Kano na da hannu wajen a cutar da wani mutum ko wasu mutane ba. Komai a nutse ya ke yi.

To, irin wannan nagarta, adalci da kuma hakuri, kunya, kara da sanin ya kamata na Marigayi Ado Bayero, su ne su ka jawo ma sa daukaka da daraja. Don haka duk wani sarki ko shugaba da ya yi irin wannan hali na Sarki Ado Bayero, zai gama lafiya. Saboda haka wajibi ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi koyi da mahaifinsa wajen gudanar da mulkin Kano.

Ga shi ’ya;yan Mai Martaba Ado Bayero guda biyu sun samu sarauta ta sarakuna masu daraja ta daya kowannensu. Wane darasi ne a cikin wannan?

To, wannan daukaka ce daga Allah kuma hakuri ba abinda ba ya kawowa. Don haka shi Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Bichi da Kano abu daya ne duk da yanzu an samu cigaba an kirkiro masarautar Bichi, wannan abin godiya ne ga Allah. A nan kuma ga Masarautar Kano, wacce Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano, to abin dai da n ake gani kuma na ke so al`umma su gane shi ne, aarki dai uban kowa ne kuma yayan kowa ne. Don haka muhimmin abu ga sarakunanmu na Kano biyar shi ne, su rungumi kowa nasu ne tunda gaba su ke da kowa.

To, kafin mu kammala wannan tattaunawa bari mu tabo siyasar kasa kasancewarka mai bin diddigin al’amuran yau da kullum, musamman siyasa da tattalin arziki. Meye ra’ayinka kan hana shigo da janareto Nijeriya?

Ra’ayina shi ne a samar da hasken wutar lantarki wadadataciya a Najeriya, domin shi injin samar da wutar lantarki duk inda ka gan shi ka ga an sa shi ko an so shi larura ce. Idan akwai wuta, ba za ka gan shi ba. Saboda haka saka dokar hana shigo da janareto kamar ya nuna ’yan majalisar kasar ba su da aikin yi ne, domin wannan magana bata lokaci ne. Idan kuwa ba haka ba, me ya sa ba za a binciko irin makudan kudaden da a ka zuba ba shekara da shekaru? Ga na zamanin Obasanjo na Dala billiyoyin 16. Ina su ke? Ina sauran kudadan da a ke magana ko yaushe? Su ya kamata a binciko, don gyaran wutar Najeriya, ba wannan maganar ba, domin an dade a na karya da yaudarar mutane kan gyaran wutar Nepa a Najeriya.

Me za ka ce kan maganar rigar kariya ga shugabannin majalisa da su ke so a ba su?Ba na goyon baya, domin zalunci ne muraran a ce ga wani mutum mai mukami, wanda ko da ya aikata laifi ba za a hukunta shi ba, sai wani lokaci idan a ka ba su, su shugabannin majalisa na dattawa ne ko na wakilai ne ko na jiha ne, to duk wanda a ka bawa, nan gaba na kasa da shi sai ya nemi a ba shi idan dai ya na da mukami na siyasa kuma yin hakan barna zai haifar a kasa, ba gyara ba tunda za a kama barawon akuya a hukunta shi kuma a kyale barawon biliyoyin Nairori, wannan zalunci ne kuma shi zalunci cikin sauri ya ke ruguza daula ko kasa. Saboda haka ba na goyan bayan sanya wa duk wani mai rike da mukamin siyasa rigar kariya a Najeriya.

A karshe wacce shawarar ka ke da ita ga shugabanni da sauran al’umma kasar?

Shawarata ga shugabanni ita ce, su su yi adalci da tsoron Allah a kowane matakin mulki tun daga kan magidanci da iyalansa da mai unguwa har zuwa sarkin yanka, daga kan kansila har zuwa shugaban kasa. Al’umma kuma ta kasance mai da’a da tarbiyya da rike sana’o’i da amana da addu’a da neman zaman lafiya a Kano, Najariya da ma duniya bakidaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: