Connect with us

RAHOTANNI

Ahlul Faidhati Sun Ziyarci Almajirin Shehu Ibrahim Inyass A Jega

Published

on

Tawagar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group bisa shugabancin Shehu Isma’il Umar Almaddah ta ziyarci raudar Almajirin Shehu Ibrahim Inyass, Shehu Balarabe Jega wanda ya rubuta shahararren littafin nan na Goran Faila.

Tun da misalin karfe 12:00 na ranar Lahadi, tawagar ta tashi daga masaukinta da ke Minanata cikin garin Sakkwato zuwa Jega, cikin Jihar Kebbi domin ziyarar mai matukar tarihi.

Tawagar ta sauka garin Jega lafiya da misalin karfe 2:00 na rana inda aka fara tarbarta a gidan Khalifan Shehu Balarabe Jega, Alhaji Yahaya bisa jagorancin shugaban masu tarbar baki, MalaMalam Abdullahi Buhari da Sarkin Malaman Jega da wasu daga cikin manyan Zawiyar Shehin da kuma kannen Khalifan bakidaya.

Jim kadan bayan gaisawa da Khalifa sai Malam Abdullahi Buhari ya gabatar da takaitaccen bayani a kan Khalifa da sauran malamai, wanda ya yi godiya, ya kuma yi yabo ga shugaban Ahlul Faidhati Mai Diwani Group, da cewa Shehi ne na Allah. Haka nan ya bayyana cewa tun da aka fara gabatar da Mauludin Shehu Ibrahim Inyass a Nijeriya shekara 36 da suka gabata, ba a taba samun wadanda suka zo ziyarar Shehin a matsayin wani bangare na Mauludin da kuma girmama Almajirancinsa ga Shehu Ibrahim ba sai Ahlul Faidhati Mai Diwani Group.

Ya kara dacewa Khalifan kani ne ga Shehu Balarabe Jega wanda ya Khalifance shi a tsawon shekara 16 na rayuwarsa. Daga bisani kuma Malam Yusha’u, ya gabatar da jawabi a madadin Khalifa domin nuna farin ciki da wannan ziyara da Ahlul Faidhati Mai Diwani Group suka kawo wa Shehu Balarabe Jega saboda Allah da kuma kara dankon zumunci na ‘Yan Faila.

Bayan gabatar da jawabai daga masu tarbar baki, Shugaban Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Shehu Isma’ila Umar Almaddah ya karanta Diwani a takaice a gaban Khalifa, sannan aka dauki hotuna gwanin ban sha’awa. Bayan kammalawa, Shehu Isma’il ya yi takaitaccen jawabi, inda ya bayyana Malam Buhari mahaifin wanda ya jagoranci tarbar baki a matsayin mataimaki ga Shehu Balarabe Jega wanda ake saduwa da shi kafin ganin Shehin.

An gabatar da sallah da cin abinci da misalin karfe 2:50 na rana, a yayin da Sayyada Fadima ‘Yar Shehu Balarabe Jegada da ‘ya’yanta suka zo don gaisawa da baki da nuna farin ciki da wannan ziyara.

An kama hanya zuwa Raudar Shehu Balarabe Jega domin ziyara. Jim kadan bayan isa gidan Shehin, an gabatar da karatun Alkur’ani mai girma da Diwani da kuma Littafin da Shehu Balarabe Jega ya rubuta na Goran Faila.

Da yake jawabi kafin shiga Raudar, Shehu Isma’il ya gode wa Ahlul Faidhati Mai Diwani Group reshen Sakkwato bisa namijin kokarinsu wurin shirya wannan ziyara mai muhimmancin gaske inda ya ce su suka tara kudinsu suka dauki nauyin komai da komai, “Aallah ya saka musu da alkhairi”.

Shehu Isma’il ya kuma yi bayanin cewa wata rana Annabi (SAW) watarana Annabi (saw) ya juyo bayan sallar la’asar kamar yadda ya zo a Hadisi, sai ya ce akwai wasu mutane da ranar alkiyama hasken fuskarsu zai rika haskawa saboda kusancinsu da Allah, sai wani Balaraben kauye ya tambaya ko su waye wadannan ya Rasulullah? Sai Annabi (SAW) ya ce mutane ne ‘ya’yan mutane da za su hadu dan Allah kuma su rabu dan Allah. A wani Hadisin kuma aka ce (mutanen) suka yi soyayya dan Allah. Shehu Isma’il ya ce duk malaman duniya in za su fassara ayar “Ala Inna auliya’al Allah…” da wannan Hadisi suke amfani, kana ya bayyana cewa “a nan mutane ne mabanbanta da muka taru dan Allah dan Bawan Allah”.

Wakazalika, Shehu tijjani ya yi bayanin cewa Shehu Tijjani mai Darikar Tijjaniyya ya yi bishara da zuwan Faila wanda a karkashin haka ya ce Faila za ta zo daga Sahabbaina wanda zai bude wa al’umma kofar sanin Allah a Musulunci da Imani da Ihsani. Manyan Sahabban Shehu Tijjani sun yi sha’awar samun Faila a hannunsu, amma daga baya da kansu suka gane ba su ba ne da ita wanda dukkan wadannan Sahabban na Shehu Tijjani Larabawa ne.

Shehu Danfodiyo (RA) ya yi nuni da bisharar zuwan Sahibul Faidhati, ya bayyana kamanninsa da jama’arshi kuma ya ce zai yawaita ziyarar Annabi (SAW). Sarki Shehu Abdullahi Bayero ya ganshi cikin falalar Allah.

Godiya ga Allah Faila ta zo a lokacin da duniya ta shiga kunci na karayar tattalin arziki, kowa zai iya bincikar tarihin ranar bakar Alhamis wanda Turawa suke ce wa ‘Black Thursday) wadda a lokacin ne Faila ta bayyana, sannu a hankali Allah ya bayyanar da falalarsa da ita.

Ya kara da cewa Annabi (SAW) a babbar kofa ta islam da Iman da Ihsan ya ajiye Shehu Ibrahim Inyass domin su daukaka da shi. Ya ce Ilimi arziki da ci gaba na duniya sun yawaita albarkar Faila.

Shehu Isma’il ya kuma bayyana cewa Littafin Goran Faila shi ne adon mu Hausawa a Faila, don haka ya yi kira da a yi riko da Goran Faila, da kuma kawar da ido ga makiya. Ya ce daya daga cikin Almajiran Shehu Ibrahim Umar Muluku ya fada masa ewa ya karanta ma Shehu Ibrahim Goran Faila yana fassara masa da Harshen Olof, inda Shehu ya yabe ta har ya yi mata ijaza, don haka duk mai son ya san abin da Faila ta kunsa da Hausa ya dauki Goran Faila ya yi ta karantawa.

Shehu Isma’il ya yi addu’ar samun zaman lafiya a kasa, daga bisani ya cika da karatun Littafin Mimiya na Shehu Malam Tijjani Kano.

Bayan kammala sallar la’asar sai aka shiga ziyara a Raudar Shehu Balarabe Jega inda aka gudanar da addu’o’i tare da ‘Yar Shehin, Sayyida Fadima wacce ya rasu ya bar ta tana da shekara tara a duniya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: