Connect with us

ADABI

Daga Littafin Bakar Guguwa (28)  

Published

on

Wane labari ne haka da sassafe?” nuni yayi mata da d’an yatsansa alamar tayi shuru kada Mummy taji murmushi tayi tare da fad’in “ok! Na gane muje” barin falon suka yi suka zagaya ta baya can wajen window’n kitchen sannan suka tsaya yana yi yana dube-dube gudun kada wani yaji me zasu ce sai da ya tabbatar babu kowa a wajen sannan ya fara magana “Yauwa ina wannan k’awar taki?” tunda ya fara magana ta gane me yake son cewa dariya Zarah tayi tana tsokanarsa “lallai Ya Imran ka kamu da son jamila tunda gashi har ka kasa bacci ka kasa danne zuciyarka ka furtan” kallonta yayi yana murmushi tare  da yi mata nuni da hannu alamar tayi k’asa da muryarta kada wani ya jiyo su cikin murya k’asa-k’asa yake magana “eh naji d’in gwara na sanar da wuri ba sai wani ya rugani ba nazo ina dana sani, ki samu ki shawo mun kanta kinji k’anwata, idan har kika yi mun hakan zan baki kyauta mai tsoka” Zarah tace “zan sanar mata nasan ma ba wanda ya ruga amma dai zan tambayeta kasan Hausawa na cewa dai-dan wani karka taccen wani, ni kuma zanyi k’ok’ari ta amince ko dan a bani babbar kyauta” dariyar jin dad’i yayi tare da fad’in “yauwa k’anwata kyautar ki mai tsokace ce” duk kaninsu suka yi dariya duk wannan abun da suke Hajjiya Usaina na kallonsu ta window’n kitchen kuma tana jinsu dariya itama tayi kawai.

Daga nan suka wuce suka tafi, tun kan Imran ya k’arasa yaci karo da Abbansu take yaja dogon numfashi fatansa Allah sa dai be jisu ba a tsorace ya durk’usa k’asa kamar mara gaskiya yace “Abbah ina kwana?” “lafiya lau har ka tashi da wuri haka?” sosa k’eya ya runk’a yi yana murmushi Alhaji yaci gaba da magana “ni yanzu futa zanyi idan ka shirya akwai maganar da zamu yi  sai kazo office ka same ni” gaban Imran ne ya yanke ya fad’i shikkenan Abbah yaji abinda muka tattauna,  zuciyarsa ce ta raya masa haka. Daga can kuma Alhaji yace ko da yake bash-shi mayi maganar daga baya” imran yaja dogon ajjiyar zuciya shikkenan Abbah ya gama jin komai ya fad’a a zuciyarsa a sanyaye ya mik’e yana niyyar wucewa bayan yace “adawo lafiya Abbah” amsa Alhaji yayi dai-dai lokacin da Hajjiya Usaina ta fito hannunta ruk’e da jakar Alhaji tana ta faman sauri zai shiga motar da Habu driber ya bud’e masa kenan ya hango Hajjiya Usaina na tafe ganin hakan yasa yaja ya tsaya ya fasa shiga har sai da ta k’araso inda yake, tana isowa ta saki murmushi a hankali tace “ina can ina Sauri na jiyo har kayi waje ga jakar dan nasan har ka manta da ita” dariya yayi “kin san kuwa na manta ba dan kin kawon ba” karb’ar jakar yayi sannan yace mata “zan wuce wajen nasa in yaso yadda muka yi da shi zan sanar miki dan ni da niyyata na aiki yaron nan yaje sai kuma naga gwara ni d’in naje yanzu da kaina nasan zan same shi tunda safiya ce ba rana ba” Hajiya tace “gwara kaje da kan naka sai yafi a mutunce” “nima abinda na gani kenan” daga nan suka yi sallama da Alhaji tare da addu’o’in samun nasara irin wanda kowacce mace takewa mijinta da zarar zai futa nan dai ya shiga cikin motar ya zauna driber yaja suka futa.

Komawa Hajjiya tayi bayan da suka ja motar,  furta Alhaji da komawar Hajjiya keda wuya Safiya ta shigo gidan ranta a b’ace ta k’arasa ciki tana isa falo ta fara fad’a “yanzu a rasa wanda zai fito ya amsa sallamar da nake ta rafkawa” a tsorace Hajjiya Usaina ta fito “sannu da zuwa yaya” wata muguwar harara ta wurga mata cikin zafin rai tace “daman kina nan amma nake ta rafka sallama kika yi shuru? Sabida rashin mutunci, ina yake shi d’an uwan nawa?” sosai Hajjiya Usaina ta kalleta wai me yasa wannan matar take da son nuna isa, kodan taga gidan k’aninta ne? Nifa na tsani irin wannan halin, a zuciyarta take fad’ar hakan, ganin  yadda take yi mata magana cikin fad’a-fad’a kamar ita ta haifeta yasa ran Hajjiya Usaina b’aci tace “ya futa yanzu” daga nan bata k’ara magana ba ta fuce ta koma sashin ta ta barta nan tsaye a falo, daman ko zama bata yi ba ganin ta barta tsaye yasa ta k’ara jin zafi da tafarfasa da kuma tsananin bak’in ciki cikin zuciya tayi kwafa ta futa babu wanda ya saurareta tare da fad’in “zan dad’a dawowa zanzo na same shi”.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: