Connect with us

LABARAI

Ginin Babbar Kasuwar Jos: An Nemi Gwamna Lalong Ya Hada Hannu Da Yan Kasuwa

Published

on

Ganin yadda gini babbar kasuwar Jos da ta kone a shekarar Alif 2002, ke tafiyar hawainiya, an bukaci gwamnatin jihar Filato, da ta hada hannu da manyan ‘yan kasuwa na ciki da wajen kasar nan wajen tafiyar da aikin ginin don a sami kamala aikin a cikin lokaci.

Daya daga cikin yan Kasuwan da suke dokin ganin an kamala ginin kasuwar a cikin dan kankanin lokaci Alhaji Iliyasu Muhammad, ne ya yi wannan kira a lokacinda yake tofa albarkacin bakinsa yadda aikin ginin kasuwar ke gudana. Ya ce kamata ya yi gwamnatin jihar ta jawo hankalin yan kasuwa su zuba jarinsu a wajen ginin kasuwar inda ya ce hakan zai sa a sami nasarar kammala ginin kasuwar a cikin gajeren lokaci kamar yadda ake bukata.

Haka nan ya kara yaba wa Gwamnan bisa ayyukan gyaran Tituna cikin garin Jos da kewaye kuma ya bukace shi da ya fadada aikin zuwa gyaran layukan da ke daura da kasuwar, kana ya ce hakan zai kara farfafa kasuwanci ciki dawajen kasuwar idan aka kammal gininta.

Alhaji Iliyasu Muhammad wanda shi ne shugaban ‘yan kasuwa masu sayar da Buhunan ‘BAKO” na kasa rashen jihar Filato, ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga al’umar jihar dasu kauda nuna bambanci Siyasa, addini da kabilanci, su hada kai su baiwa Gwamnan jihar Rt. Honarabul Simon Bako Lalong, cikakken hadin kai da goyon baya don ya sami kwarin guiwar kamala ayyukan da ke gabansa kafin karshen wa’adin mulkinsa na biyu a Alif 2023.

Ya yaba wa Gwamnan bisa  dimbin nasara da gwamnati maici yanzu karkashin jagorancinsa ta samu wajen maido ingantaccen  tsaro da zaman lafiya a jihar a cikin dan kankanin lokaci da hawansa mulkin jihar.

Ya ce a ‘yan shekarun da suka gabata Allah ya jarrabi jihar Filato da rikicin addini, Kabilanci da siyasa amma da hawan kujerar mulkin jihar a Alif 2015, ya sami nasara wajen hada kawunan mutanen da da sabani ya shiga sakaninsu, hakan ya ce ya haifar da ingantattaccen zaman lafiya da kyakkawar dangantaka a tsakanin al’ummar jihar.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: