Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Gudanar Da Taron Tattauna Matsalolin Tsaron Yankunan

Published

on

Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yammacin Kasar nan tare da Gwamnan Jihar Neja, a ranar Larabar da ta gabata suka zauna karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, wanda ya bayyana aniyarsu ta duba halin da tsaro ke ciki a jihohin nasu, kamar yadda Daraktan Yada Labaran Mataimakin Gwamnnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge ya shaida wa Jaridar LEADERSHIP A YAU.

Gwamnonin, wadannan jihohin nasu ke yin aiki tare domin duba abubuwan da akagudanar a kokarin da suke yi na magance matsalar garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma manyan laifuka wadanda ke faruwa a yankunansu tare da samarda tsare-tsaren da za a aiwatar domin magance wadannan matsaloli.

Taron wanda ya gudana a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Fadar GwamnatinJihar Kaduna, wanda shi ma Gwamnan na Kaduna ya samu damar halarta tare daGwaman Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Dakta Nasiru Yuisf Gawuna.

Haka zalika, cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu, Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan Zamfara Alhaji Bello Muhammad da Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani Bello.

Bayan taron tattaunawar tare da Shugabannin Hukumomin tsaro, manyan Jami’an tsaro, Sakatarorin Gwamnatocin Jihohi da mashawarta kan harkokin tsaro, Gwamnonin Jihohin 9, sun amince da kara inganta matakan ma-gance matsalar fashi da makami tare da dakile yaduwar cutar Corobirus.

A cikin jawabin bayan taron da Shugaban Muryar Gwamnoni ya gabatar, Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, Gwamnonin Jihaohin ciki har da Gwamnan Jihar Kwara, sun amince da hada karfi domin samar da mafita kan ayyukan harkokin tsaro, domin gaggauta magance matsalar aikata miyagun laifuka.

Gwamnonin sun kuma amince da hada karfi wajen kare al’ummarsu daga kamuwa da cutar Cobid-19. Wannan a cewar jawabin bayan taron, akwai ru-fe makarantu cikin matakan da za a dauka a kowace jiha tare da gudanar da cikakken bincike na tsawon kwanaki 30 da ake fatan farawa daga ranar Litinin mai zuwa 23 ga watan Mayun, 2020.

Haka kuma daga cikin matakan da za a dauka domin dakile yaduwar cutar ta Coranabirus, wanda jihohin za su dauka, akwai gudanar da gangamin wayar da akai domin kaucewa duk wasu tarukan da jama’a masu yawa kan taru har zuwa wani lokaci.

Na uku kuma, akwai gangamin wayar da kai daga Jami’an lafiya, kowace jiha za ta cigaba da aiwatar da gagarumin gangami, domin karfafawa jama’a gui-war cigaba da tsaftace jiki, wanda ya hada da wanke hannu da kuma tsaftace muhallinsu,” in ji sanarwar.

Shugaban Muryar Gwamnonin Arewa Maso Yamman, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana godiyarsu ga Gwamnan Jihar Kaduna da sauran al’ummar Jihar bisa karbar bakuncin wannan muhimmin taro da suka yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: