Connect with us

RAHOTANNI

‘Huldar Kasuwanci Da NPA Ya Fi Ko Ina Sauki A Afrika Ta Yamma’

Published

on

Koma bayan rade-radin da wasu al’umma ke yadawa, farashin huldar kasuwanci da hukumar tashoshin jiragen ruwan Nijeriya NPA ba shi ba ne mafi tsada a yankin Afrika ta yamma ba, maimakon haka ma bincike ya nuna cewa, farashin da ake samu a NPA shi ne mafi sauki a yankin Afrika ta Yamma.
Wannan bayanin ya fito ne daga takardar sanarwar da Manaja mai lula yada labarai na hukumar Mista Jatto A Adams ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Legas.
Sanarwa ta kuma ci gaba da cewa, a watan Mayu na shekarar 2019, kamfanin Messers Crown wadda hukumar ta dauka suka kuma gudanar da aiki tare da tallafin hukumar UK Aid sun gudanar da cikakken bincike in da suka bayar da rahoton dake nuna cewa huldar kasuwancci da hukumar NPA ya fi sauki kwarai da gaske akan abin a ke samu a kasashen Ghana da Togo da sauran kasashen yankin Afrika ta yamma.
Rahoton ya nuna cewa, misali yayin da ake chajin Dala 94,567.63 ciki har da kudin harajin VAT wajen zirga-zirgar sudukan jiragen ruwa, ana kuma chajin kudin GRT 26,770, yayin da kuma ake karbar Miliyan 196 akan jirgin dakwan kaya mai MT 14,100 a Nijeriya, a tashoshin jiragen ruwa na kasashen Ghana da Togo ba haka abin yake ba, a can suna karbar Dala 217,879.07 da Dala 120, 357.58 ciki har da kudin harajin VAT akan ayyuka akan jiragen ruwan kamar dai yadda NPA ta samar, wanda hakan yana nuna cewa, na NPA ya fi sauki da nisan gaske.
Haka kuma yayin da NPA ke chajin Dala 108, 806.90 ciki har da harajin VAT akan zirga-zirga da jirigin ruwa mai dauke da kwantaina mai GRT 39,906 da LOA na Miliyan 261 dake da tsawo da fadin 172×20” da kuma 139×40”, a tashoshin kasar Ghana da Togo su kudaden da suke karba ya kai Dala 117,906.58 da kuma Dala 128,406.94 ciki har da harajin VAT.
‘Haka kuma hukumar na sanar da al’umma musamman masu hulda da NPA cewa, bata janye kudaden da ake chaja na Towage ba, wanda aka sake fasalisan a shekarar 2015, bamu sake fasalin kudaden harkokin da muke gabatarwa ba tun yadda yake a shekarar 1993. Haka kuma na faruwa ne duk da yadda aka sanya chajin STEVEDORING a cikin jadawalin ayyukanmu a bisa kuskure, wanda masu gudanar da wani bangare na tashar ke karba da suna hukumar. Ya kuma kamata a fahinci cewa, kudaden da ake karba na wasu ayyukan da ake gabatarwa ba suna cikin hurumin hukumar NPA bane, kuma hukumar bata da karfin sauya fasalin yadda ake gudanar da harkokin tattalin arziki a tashar jiragen ruwan Nijeriya kai tsaye.
Hukumar tashar jiragen ruwa Nijeiya na sanar da al’umma musamma masu hulda da ita cewa, ta na nan a kan bakan ta na samar da yanayi mai tsafta na gudanar da ayyuka a tashoshin jiragen ruwa Nijeriya, haka kuma na daga cikin kudurorin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na samar da yanayin gudanar da kasuwanci ta hanyar karfafa gasa a tsakanin tashoshin jiragen ruwan Nijeria, wannan nasarar yana kuma cikin kokarin shugabar hukumar, Hajiya Hadiza Bala Usman ta yi ne na sake fasalin hukumar tun lokacin da ta hau karagar mulkin shugabancin hukumar, yana kuma cikin abubuwan da Shugaba Buhari ya lura dasu wajen sake nada ta a msatsayin shugabar hukumar a karo na biyu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: