Connect with us

WASANNI

Idan Coronavirus Ba Ta Zo Wajena Ba Ni Zan Je Inda Ta Ke, Cewar Ibrahimovic

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, ya kaddamar da gidauniyar neman taimako domin yakar annobar cutar coronavirus sannan dan wasan ya kuma nemi sauran takwarorinsa da ke buga kwallo a fadin duniya da su hada hannu domin korar wannan cuta.

Dan kwallon dai yana buga wasa ne a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan a Italiya, kasar da coronavirus ta fi yi wa illa bayan China bayan da kullum ake sake samun karin wadanda ke kamuwa da cutar da wadanda ke mutuwa.

Yanzu dai Ibrahimovic ya tara kudi da suka kai euro 50,000 sau biyu haka kuma Ibrahimovic ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa Italiya ta yi masa komai, a wannan lokacin mara dadi yana so ya biya wannan kasa da yake so abin da ta yi masa.

A ranar Litinin ne shima dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba ya kaddamar da irin wannan asusun neman tallafin duk a kan wannan cuta inda yace zai ninka abinda aka hada domin tallafawa duniya.

“Ina fatan abokan kwallona za su taimake ni a kowanne bangare na wasanni wadanda za su bayar da kadan ko mai yawa duk su taimaka a kori wannan cuta wadda take kashe al’umma kullum” in ji dan wasa Paul Pogba.

Ya ci gaba da cewa “Mu hada hannu wajen taimakon asibitoci da likitoci da kuma ma’aikatan asibiti wadanda ba sa gajiya wajen kokarin ceton rayuwarmu saboda a yau mu muke yaba musu sannan mu hada hannu wuri daya domin yakar wannan cuta mu yi nasara a wasan!”

Sa’a guda bayan Ibrahimovic ya wallafa wannan sanarwa kudin da aka samu suka karu zuwa euro 109,652, kwatankwacin fam 100,999 sannan a karshen bidiyon da ya wallafa ya ce “ku tuna idan wannan cuta bata je wajen Zlatan ba, Zlatan zai je wurin ta!”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: