Connect with us

WASANNI

Karshen Zaman Pogba Ya Zo A Manchester United

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa Manchester United zata rage farashin dan wasa Paul Pogba ya koma fam miliyan 100 domin ganin kungiyoyin da suke zawarcinsa sun samu da-mar sayansa a kakar wasa mai zuwa.

Tun a farkon wannan kakar ne dai dan wasa Paul Pogba ya bayyana aniyarsa ta barin Manchester United ya yinda kungiyar kuma ta bayyana cewa dan wasan bana sayarwa bane saboda tana fama da karancin ‘yan wasa.

Sai dai kawo yanzu bayan da kungiyar ta dauki sabon dan wasan tsakiya, Bruno Fernandez, wanda tun bayan zuwansa Manchester United tauraruwarsa take haskawa aka fara bayyana cewa kungiyar zata iya rabuwa da Pogba.

Kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ce a halin yanzu wadda har yanzu take bibiyara tsohon dan wasan nata wanda ta sayarwa da United din a shekara ta 2016 akan kudi fam miliyan 89 kuma a shirye take data sake mayar dashi kasar Italiyan da buga wasa.

Sai dai itama kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ma har yanzu tana ci gaba da bibiyar dan wa-san dan kasar Faransa wanda kociyan kungiyar, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa yana fatan suyi aiki tare a Real Madrid.

A kwanakin baya ne dai wakilin dan wasan Mino Raiola, ya bayyana cewa dan wasan zai iya sake komawa kasar Italiya da buga wasa sai dai ya ce ba zaiyi masa dole akan inda yake son buga wasa ba.

Kawo yanzu dai wasanni bakwai kawai Pogba ya bugawa Manchester United a wannan kakar wasan sakamakon ciwon da yake ji sai dai an shirya zai dawo a wannan satin amma sakamakon dage wasanni yasa dawowar tasa aka jinkirta sai ranar da aka koma buga wasanni.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: