Connect with us

LABARAI

Gwamnan Gombe Ya Nuna Farin Ciki Da Zaman Mal. Murtala Sakatare Janar Na ACF  

Published

on

Gwamnatin Jihar Gombe ta nuna farin cikinta a bisa kasancewar da Malam Murtala Aliyu ya yi na zama sabon sakatare Janar na kungiyar Dattawan Arewa wato ‘Arewa Consultatibe Forum’, ACF. Har-ila-yau, an kuma misalta kungiyar Dattawan Arewan a matsayin wata jigo da ke buga-bugar samar wa yankin arewa ci gaba mai ma’ana a kowani lokaci.

A sakon taya murna da gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya ya fitar ta hannun babban mai taimaka masa kan hulda da ‘yan jarida, Ismaila Uba Misilli, Inuwa ya misalta Malam Murtala a matsayin sakatare janar na ACF a matsayin wanda ya cancanta kuma ya dace matuka da kujerar, lura da irin kokarinsa da hazakarsa ta fuskacin gwazonsa a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu. Ya ce, sabbin jagororin ACF suna zuwa ne a daidai lokacin da yankin ke gayar fuskantar matsaloli da dumbin kalubale da suka hada da matsalar tsaro, fashi da makami, rashin aiyukan yi a tsakanin matasa, da sauran matsalolin da suka shafi tattalin arziki, “Amma samuwar irinsu Malam Murtala Aliyu, da irin su Audu Ogbe, kungiyar na da cikakken dama da ikon sauke nauyin da ake bukata,” A cewar gwamnan.

Gwamna Yahaya ya nuna cewar kujerar sakatare janar babban kujerace wacce yake da cikakken dama da ikon sauya abubuwa da daman gaske, sai ya shawarceshi da ya tabbatar da yin aiki da hazakarsa da kokarinsa domin kiyaye kima da tabbatar da shawo kan matsalolin da arewacin Nijeriya ke fuskanta. Gwamnan sai ya bayyana aniyar gwamnatinsa na mara wa sabbin shugabannin ACF baya domin su cimma nasarori, yana mai yi musu addu’ar samun dafawar Allah cikin harkokin da suka sanya a gaba na kokarin ciyar da yankin arewa da kasa baki daya gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: