Connect with us

LABARAI

Tsige Sarki Sanusi: Gamayyar Kungiyoyin Arewa Maso Yamma Sun Jinjina Wa Ganduje

Published

on

Kwanaki kadan bayan warware rawanin tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, wanda Gwamnatin Jihar Kano ta yi, sai ga kugiyoyi da dama daga Arewa Maso Yammacin wannan kasa, ciki har da Kungiyar Cigaban Hadin KanMatasan Arewa, suna jinjinawa kokarin Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, inda suka bayyana yin hakan a matsayin wani yunkuri na kare kima tare da martabar Masarautar Kano, kamar yadda Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar LEADEERSHIP A YAU Asabar.

Jawabin hakan, na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 17 ga watan Mayun wannan shekara, wanda jagoran kungiyar Ambasada Adamu Jikan Mani ya rattabawa hannu, mai taken ‘Takardar taya murna bisa sake fasalin Masarautar Kano’.

Sannan, sun taya Gwamna Abdullahi Umar Ganduje murna akan haka.Wasikar ta cigaba da cewa, “Muna sanar da mai girma Gwamna cewa, a matsayinmu na Kungiyar Cigaban Matasan Arewa Maso Yammacin wannan kasa (NYPU), muna cikin sahun gaba wajen bibiyar dukkanin abubuwan da suka wakana tsakanin tsohon Sarkin Kano da kuma Ofishin Gwamnatin Jihar Kano.”

Muna farin ciki da wannan mataki, “Mun gamsu da kokarinka na kare kimar Masarautar Kano, mun kuma dauki hakan ne a matsayin wata gagarumar nasara, ba wai ga Gwamnan Kano ba, har ma da daukacin al’ummar jihar, Masarautar Kano da ma daukacin Arewacin Nijeriya baki-daya. Babu shakka, wannan ba karamin hobbasa ba ne ta dukkanin bangaren da mutum ya kalli wannan al’amari.”

Wasikar ta cigaba da cewa, “mun gamsu da kokarin Gwamna Ganduje na yunkurin daga darajar Jihar Kano zuwa mataki na gaba.” Hakan kuma, ya kara tabbatar lokacin da muryar Gwamnonin APC suka bayyana Gwamna Ganduje, a matsayin wanda ya zarta sauran ta fuskar ayyukan raya kasa. Don haka, muna kara jinjinawa Gwamna bisa samun wannan nasara, wanda hakan ke tabbatar da kyakkyawan jagorancinsa, da wannan kuma ya kara wa kansa wata kima da daraja.” a cewar takardar.

A karshe kuma suka bayyana cewa, “daukacin Matasan Arewa Maso Yammacin wannan kasa, muna yi maka fatan alhairi tare da fatan samun dukkanin nasarorin da ka sanya a gaba. Muna kara taya ka murnar wannan gagarumar nasara, tare da fatan cigaba da samun irin wannan nasara a dukkanin rayuwarka.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: