Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Yadda Likitocin Kasar Sin Wadanda Suka Shiga Ayyukan Yaki Da Cutar COVID-19 A Duniya Suka Samu Amincewa Sosai

Published

on

Yanzu haka annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa a sassa daban daban na duniya. Likitocin kasar Sin da dama da suka shiga ayyukan yaki da cutar a kasar sun tafi ketare domin taimakawa takwarorinsu na kasashen waje, ko kuma sun yi karin bayani kan fasahohin yaki da cutar cikin hoton bidiyo kan Internet. Kyawawan halayen likitocin kasar Sin da yadda suke gudanar da ayyukansu, sun samu amincewa daga sassa daban daban na duniya.

A ranar 19 ga watan nan, Zhong Nanshan, Madam Li Lanjuan, da wasu kwararrun kasar Sin da suka shahara a duniya sun yi karin bayani filla-filla ga takwarorinsu na kasashen ketare kan fasahohin kasar Sin wajen yaki da cutar ta COVID-19 a yayin taron musayar fasahohin yaki da cutar na duniya, wanda aka gudanar ta kafar Internet.
Daya daga cikin hanyoyin da kasar Sin ta yi amfani da su wajen dakile yaduwar cutar cikin hanzari shi ne, gaggauta yanke shawara kan ko wani ya kamu da cutar ko a’a, da ba shi magani bisa yanayin lafiyarsa. A cikin takardar jagora kan kandagarki da dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 da aka sake wallafawa karo na 7, kasar Sin ta yi cikakken bayani kan yadda take yaki da annobar ba tare da rufa-rufa ba.
Kwanan baya, shugabannin wasu kasashe, ciki har da na kasar Czech, sun nuna wa kasar Sin godiya tare da fatan koyon fasahohin Sin don hana yaduwar annobar a kasashensu. Sa’an nan kuma, masu amfani da Internet a sassa daban daban na duniya sun jinjina wa likitocin kasar Sin, tare da bayyana su a matsayin jarumai na hakika. (Mai Fassarawa: Tasallah Yuan)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: