Connect with us

RAHOTANNI

An Karrama Babban Jojin Katsina Danladi Abubakar

Published

on

An hori yan’jarida a jihar Katsina akan yadda labaran kanzon kurege wanda suke sa fargaba a zukatan al’umma.

Babban jojin jiha mai shari’a Musa danladi Abubakar yayi wannan kira a lokacin da ya karbi wata lambar yabo wadda jaridar Almizan ta karramashi da ita.
Ya bukaci yan’jarida da su mayar da hankalinsu akan ciyar da jiha gaba da kuma gaskiya a cikin aikinsu.
Mai shari’a Musa danladi Abubakar ya shawarci ‘yanjarida dasu guji halayyar nan ta yada labaran kanzon kurege kamar yadda ake yadasu a kafar sadarwa ta zamani.
Ya kuma bukaci al’umma dasu rungumi sasanci a tsakani a matsayin hanya mafi kyau kafin su tafi kotu.
Babban jojin ya kuma godema jaridar Almizan tunda farko shugaban NUJ na jihar Katsina kwamral Tukur Hassan dan-Ali ya bayyana karramawar a matsayin wadda ta dace da shi.
A nashi jawabi, wakilin jaridar Almizan Mal. danjuma Katsina yace zabar mai shari’a Musa danladi Abubakar ya zamo sakamakon gudummuwar da yake bayarwa game da cigaban harkar watsa labarai da kuma al’umma baki daya
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: