Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Bankin BOA Ya Samu Biliyoyin Nairori Don Tallafi A Gwamnatin Buhari – Dr. Dahiru Bala

Published

on

A ranar Litinin da ta gabata ne, Babbana Manajan Rukunin Bankin BOA, mai kula da Jihar Kano da Jigawa, Dakta dahiru Bala ya bayyana cewa, a wannan lokaci na Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, manyan Bankunan kasashen Waje kamar kasar Amurka da Ingila da kuma Bankin Raya Afirka, wato A.D.B tare da wasu Jihohin Nijeriya guda bakwai, sun yarda tare da yabawa kokarin Bankinsu na B.O.A, musamman ta fuskar bayar da da tallafi domin bunkasa Kamfanoni da Masanaantu a Najeriya, sakamakon kudirin da Gwamnatin Nijeriyar ke da shi na farfado da harkokin Noma, Kamfanoni da kuma Masanaantu a daidai wannan lokaci.

Kazalika, sun bayar da makudan biliyoyin Nairori domin agazawa masu son kafa Kamfanoni da Masanaantu, a matsayin wani tallafi na musamman daga wannan Gwamnati ta Shugaba Buhari, domin farfado da tattalin arzikin Nijeriya baki-daya, in ji shi.
Dakta Bala, ya kara da cewa daga cikin jihohin da suka sanya hannu tare da yarjejeniyar baiwa wannan Banki na B.O.A kudi, domin tallafawa al’ummarsu sun hada da Jihar Kano, Borno Gombe, Taraba, Benue, Kaduna, Bayelsa da kuma Delta, sai kuma kasashen Turai da ya hada da Amurka da Ingila da kuma Bankin Raya Afirka.
Har ila yau, wadannan makudan kudade a cewar Daktan, wanda yawansu ya kai babu bukatar bayyana su a daidai wannan lokaci, amma dai suna nan a wannan Banki na B.O.A, ya kuma tanade su domin baiwa dukkanin wani dan Najeriya da ke son kafa Kamfani ko Masana
anta ko kuma bunkasa wanda yake  da shi.
“Babbar manufar yin hakan kuwa shi ne, idan aka samu nasarar farfado da wadannan Kamfanoni tare da Masanaantu, ko shakka babu Matasa za su samu aikin yi, sannan harkokin kasuwanni su ma za su farfado a kuma hada-hadar saye da siyarwa, wanda hakan zai kawo cikakken tsaro tare da bunkasar tattalin arziki a wannan kasa”, a cewar tasa.
Har wa yau, kadan daga cikin sharuddan karbar wannan tallafi a matsayin rance daga B.O.A  shi ne, duk mai son karba wajibi ne ya kasance yana da Kamfani, yana kuma biya wa Kamfanin nasa haraji tare da dukkanin wata alama ko shaida wacce za ta tabbatar da cewa, dan kasa na-gari ne. Idan kuma sabon Kamfani ne mutum yake son kafawa, yake kuma bukatar wannan bashi, to ya tabbata ya zo da takardu da kuma tsari na kwararru a kan irin Kamfani ko Masana
antar da yake son kafawa.
Dakta dahiru ya sake bayyana wani abu mai karfafa gwaiwa ga masu son wannan bashi, inda ya ce ba daga kafa Kamfani ko Masanaanta za ka fara biyan wannan bashi ba, wani sai an yi wata shida; wani kuma shekara guda ko ma fiye da haka. Ya danganta da irin bashin da ka karba mai yawa ne ko kuwa dan kadan ne, a nan ne za a gane lokacin da za ka fara biyan wannan bashi,  a cewar tasa.
Sannan a karshe kuma, ya shwarci al
ummar Jihar Kano da Jigawa da ma sauran al`ummar Nijeriya baki-daya, da su hanzarta kowa ya tashi tsaye ya yi da gaske ka da a yi wasa wajen yin amfani da wannan dama, domin cin gajiyar wannan tallafi da ya zo daga nan gida Nijeriya da kuma ma sauran kasashen duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: