Connect with us

WASANNI

Coronavirus Ta Yi Wa Madrid barna, Cewar Zidane

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa, cutar Coronavirus data addabi duniya ta yiwa kungiyar barna bayan tsohon shugaban kungiyar ya mutu sakamakon cutar.

Tsohon shugaban kungiyar ta Real Madrid, Lorenzo Sanz ya mutu ne a ranar Asabar bayan da ya kamu da cutar Coronavirus kuma Sanz mai shekaru 76, shi ne shugaban Real Madrid tun daga shekarar 1995 zuwa 2000, a lokacin da kungiyar ta lashe gasar zakarun Turai har sau biyu.
kasar Sipaniya tana daya daga cikin kasashen da suke fama da cutar ta Coronavirus a nahiyar turai bayan kasar Italiya kuma har yanzu tana ci gaba da kama mutane sannan kuma ana ci gaba da mutuwa a dalilin cutar.
“Coronavirus tayi mana illa babba saboda ta dauke mana wani jigo acikin wannan kungiyar wanda tarihin wannan kungiyar bazai rubutu ba ba tare da sunansa ba tabbas munji zafin mutuwar Sanz” in ji Zidane
Ya ci gaba da cewa “Ba kawai Real Madrid ba manyan kungiyoyi da manyan ‘yan wasa a duniya sunyi takaicin mutuwarsa sai dai ba zamu iya komai ba saboda ita mutuwa ba’a iya dakatar da ita idan tazo sai an tafi”
Sanz ne ya sayo manyan ‘yan wasa irinsu Roberto Carlos, Clarence Seedorf da kuma Dabor Suker a lokacin da yake jan ragama a Real Madrid sannan kuma ya kasance shugaban da magoya bayan kungiyar ba zasu taba mantawa dashi ba.
Ya fadi zaben shugabancin kungiyar a takara tsakaninsa da Florentino Perez a shekara ta 2000 wanda tun daga wannan lokacin ya koma gefe ya ci gaba da kallon yadda ake gudanar da kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: