Connect with us

LABARAI

Covid-19: Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa Ta Ce Ma’aikatanta Su Yi Aiki Daga Gida

Published

on

Hukumar gudanarwa NPA ta umarci wasu bangaren ma’aikatanta su yi aiki
daga gida na tsawon kwanaki 14, a matsayin wani mataki na dakile
yaduwa cutar coronavirus da ake fama da ita a fadin duniya.
Bayanin haka ya na kunshe ne a takardar sanarwa da ta fito daga
shugabar hukumar, Hajiya Hadiza Bala Usman ranar 23 ga watan Maris
2020 aka kuma raba wa manema labarai a Legas.
Hajiya Bala Usman ta ce, ma’aikata a sashen da suka hada Marine da
Operations da Health da Safety da Environment da Security da kuma
Finance za su ci gaba da zuwa aiki kamar yadda suka saba.
“Sakamakon barkewar cutar coronavirus an umarci ma’aikata a wadannan
bangarorin su kasance a gida na tsawon kwanaki 14 daga ranar 23 ga
watan Maris 2020.
“Ana kuma shawartar ma’aikatan su dauki matakan kare kansu kamar yadda
likitoci suka bayar da shawara don kare kansu da na sauran al’umma.
“An kuma shawartar dukkan ma’aikata su rungumi wannan shirin da
mahimanci,” inji ta.
Daga nan ta kuma bayyana bangare da wanna shirin ya shafa da suka hada
da bangaren ’Corporate and Strategic Communications inda ya sha fi
ma’iakata daga mataki na JSS3 zuwa MSS4, da ‘Audit Division’ ma’aikata
daga mataki na JSS3 zuwa SSS1, ‘Legal Services/Board’ ma’aikata daga
mataki na JSS3 zuwa MSS4, ‘Corporate and Strategic Planning’ ma’aikata
daga mataki na JSS3 zuwa MSS4.
Sauran sun kuma hada da ma’aikata a ofishin shugaban hukumar ‘Managing
Director office’ ma’aikata daga mataki JSS3 zuwa MSS4, sai kuma
‘Monitoring and Regulatory Services’ ma’aikata daga mataki na JSS3
zuwa MSS4, da ‘SERVICOM: Staff’ ma’aikata daga mataki na ‘JSS3 zuwa
MSS4 da ‘Public Private Partnership’ ma’aikata daga mataki na JSS3
zuwa MSS4. Haka kuma ma’aikata dake aiki a ofishinmu na Abuja masu
mataki na JSS3 zuwa SSS1 da kuma bangaren ‘Human Resources’ ma’aikata
masu matakin albashi na JSS3 zuwa MSS4 duk za su kasance a gida na
stawon kanaki 14.
Haka kuma an bayyana cewa, ma’aikata daga bangaren gudanarwa
(Administration) masu mataki na JSS3 zuwa MSS4, da ‘Engineering’ masu
mataki na JSS3 zuwa MSS4,da ‘Land and Assets Administration’ masu
maraki na JSS3 zuwa MSS4, da ‘Enterprise Risk Management’ ma’aikata
masu mataki na ‘JSS3 zuwa MSS4 da kuma ma;aikatan dake bangaren
‘Superannuation and Investment’ masu matakin JSS3 zuwa MSS4.
Shugabar hukumar Hajiya Hadiza Bala Usman ta shawarci dukkan
ma’aikatan hukumar su yi aiki da wannan jadawalin kamar yadda aka
tsara don tabbatar da lafiyar al’umma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: