Connect with us

WASANNI

Fellaini Na Samun Sauki Daga Coronavirus

Published

on

Dan wasa Maroune Fellaini ya bayyana cewa tun bayan da likitoci su ka tabbatar yana dauke da cutar Coronavirus ya ke bin ka’idoji da abinda a ka gaya ma sa, domin ganin ya samu damar warkewa daga cutar.

A ranar Asabar ne a ka tabbatar da cewar tsohon dan kwallon Manchester United, Marouane Fellaini, ya kamu da cutar Coronavirus kuma ya shiga jerin ‘yan wasan kwallon kafa a duniya da su ka kamu da cutar.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, dan wasan mai shekaru 32 wanda ke buga wasa a kungiyar Shandong Luneng ta kasar China, ya ce, ya na sa ran ya koma buga kwallo da zarar ya warke.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na China sun ce Fellaini yana can a kadaice a wani asibiti mai suna Jinan kuma yana samun sauki sai dai shima dan wasan da kansa ya bayyana cewa yana ci gaba da murmurewa.
“Ina samun sauki yadda yakamata domin duk abinda likitoci suka gayamin ina kiyayewa saboda haka ina samun sauki zan koma fili domin ci gaba da buga kwallo sai dai a halin yanzu ina bukatar addu’a” in ji Fellaini
dan kwallon Belgium din ya koma China ne a shekara ta 2019, bayan shafe shekaru 11 a gasar Firimiya ta Ingila tare da Manchester United da Eberton sannan yana bugawa tawagar ‘yan wasan kasar Belgium wasa.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce Gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa dan wasansu Fellaini ya kamu da cutar sai dai tuni hukumomin kungiyar suka dauki matakin daya kamata domin ganin cewa bai shafawa ragowar ‘yan wasan kungiyar ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: