Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnan Katsina Ya Yi Bayani Kan Cutar Covid-19

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta kara wasu tsare tsare na fadakar da al’umma kan batun cutar kurano birus dake yaduwa a kasashen duniya, ciki har da Najeriya.

Gwamnan jihar Katsina Alh. Aminu Bello Masari, ya gana da wasu masu ruwa da tsaki domin ganin an cimma nasarar abinda a ka kudurta.
Daga cikin wadanda gwamnan ya gana da su sun hada da kwamishinan watsa labarai na jihar Katsina Alhaji Abdulkarim Yahaya Sirika, PS na ma’aikatar lafiya, daya wakilci kwamishinan Dr. Kabir Mustapha da DG Media Abdul Labaran Malumfashi.
Kazalika, akwai GM gidan rediyo Mal. Sani Bala Kabomo da ya samu wakilcin daraktan sashen labarai da lamurran yau da kullum na gidan rediyon Mal. Hassan Bako, da GM na KTTb, Sani Garba Kuringafa.
A wani bangare na fadakar da daukacin al’ummar jihar, gwamna Masari, zai yiwa mutane jawabi ta kafafen watsa labarai da karfe (8) na daren lahadi.
A daya hannun ma, gidan rediyon jihar Katsina da KTTb, zasu hada wani shiri na musamman don tattauna batutuwa da zai zo da misalign karfe 10-12 na daren lahadi.
Ana kyautata zaton kwamishinan watsa labarai P.S na ma’aikatar lafiya babban likitan asibitin kwararri na Katsina da shugaban hukumar kula da lafiya daga tushe na jihar Katsina, da Mal. Bashir R/Godiya su halarci shirin don bada gudummuwa.
Shirin dai zai fadakar da mutane kan yunkurin gwamnati na dakile yaduwar cutar corona birus.
Gwamnan kuma ya gana da manema labarai dukkanin irin yadda tsarin ke gudana domin ganin haka ta cimma ruwa ta yadda za’a shawo kan al’amarin kota kwana game da wannan cuta dake yaduwa tsakanin al’umma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: