Connect with us

LABARAI

Limamin Kirista Ya Yi Shahada Lokacin Jagorantar Ibada

Published

on

Wani abin firgici da ban tsoro ya auku a ranar Lahadin nan da ta gabata a Cocin, Parish priest na Saint Helen’s Catholic Church, Ogbogoro, inda babban Limamin Cocin da ke jagorantar addu’a a Cocin Rebaran Fr. Simeon Kuro, kawai aka ga ya murmure kasa ya fadi a nan take kuma ya ce ga garinku nan.

An ce lamarin ya auku ne a daidai lokacin da Rabaran Kuro yake gabatar da addu’a a Cocin wanda yake a karamar hukumar Obio/Akpor, ta Jihar Ribas.
Matashin Limamin na Kirista an yi kokarin garzayawa da shi Asibitin koyarwa na Jami’ar Fatakwal, amma ko kafin a kai ko’ina aka shelanta mutuwar na shi.
Majiyar tana cewa, “Ina mai tabbbatar maku da cewa babban Limamin Cocin, St. Helen’s Catholic Church, Reb. Fr. Simeon Kuro, ya fadi ya mace a ranar Lahadi lokacin da yake gabatar da addu’o’I a Cocin.
“An kuma garzaya da shi zuwa Asibitin koyarwa na Jami’ar Fatakwal da misalin karfe 10:30 na safiya, amma ko kafin a kai ko’ina sai aka shelanta mutuwar na shi.
Wata majiya a Asibitin koyarwar ta tabbatar da mutuwar na shi.
A lokacin da wakilinmu ya tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar, Mista Nnamdi Omoni, cewa ya yi ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba daga babban jami’in ‘yan sanda na yankin.
Da wakilin namu ya tuntubi daraktan sadarwa na Cocin, Catholic Diocese da ke Fatakwal, Rabaran Fr. Francis Tete, cewa ya yi ba zai iya yin magana a kan lamarin ba a halin yanzun.
Sai dai , ya shaida wa wakilin namu cewa zai yi magana ne da zaran hukumomi sun ba shi izinin yin maganan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: