Connect with us

LABARAI

Makarantar Nuruddinil Islam Ta Yaye dalibai 214 A Kano

Published

on

Makarantar Islamiyya ta Nuruddinil Islam Watahfizul kurAni Karim, karkashen Shugabancin Mallam Yahaya Dauda, wanda aka fi sani da Mallam Gambo da ke Unguwar Tudun Fulani Kurnan Asabe, cikin karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano, ta yi bikin walimar yaye dalibai 214, wanda  26 daga cikinsu Allah Ya azurta su da haddace littafin Allah wato, Alkurani mai girma, daga cikin mahaddata 26 akwai maza takwas, sai kuma mata 18, wadanda Allah Ya azurta da haddar Alkurani mai girma, 180 kuma su ne wadanda suka yi saukar karshe kamar dai yadda Shugaban Makarantar Mallam Gambo, ya tabbatar da hakan a wurin walimar da aka gabatar a harabar makarantar da ke Unguwar Tudun Fulani, a ranar Asabar da ta gabata.
Haka kuma, ya bayyana cewa wannan sauka ita ce karo na takwas daga lokacin da aka kafa makarantar a shekarar 2005, da Malami guda daya tak da kuma dalibai ‘yan kadan, wanda yanzu haka kimanin dalibai 2000 aka yaye a irin wannan tsari da makarantar ta ke da shi. Sannan ya kara cewa, suna hada kai  a tsakanin Malaman makarantar da iyayen yara wajan ganin yaransu sun samu ingantaccen ilimi tare da tarbiyya musamman bisa la
akari da wayar hannu a wannan zamani ta zama alakakai wajen ruguza tarbiyya idan ba a lura ba.
Haka nan, ya kuma yabawa daukacin Malaman makarantar da iyayen dalibai da sauran mutanen Unguwar maza da mata, musamman Malamai Shugabanni da sauran mawadata da suke ba da gudunmawar hadin kai da sauran makamantansu, domin cigaban wannan makaranta tare da shan alwashin cigaba da cusa tarbiyya,  da`a da kuma kunya ga daliban wannan makaranta da aka ba su amanarsu.
A karshe dai, daya daga cikin iyayen daliban da suka yi wannan sauka a wannan makaranta, Alhaji Haladu Mai Jarida da Littattafai, a bakin kasuwar Bata da ke nan Kano, nuna farin cikinsa ya yi ga Allah madaukakin Sarki, da ya nuna musu wannan rana mai tarin albarka, inda kuma ya yaba wa Mallam Gambo da sauran Malamai kan hakuri da juriya da suke yi wajen daukar dawainiyyar ’ya’yanmu da su ke koyarwa. Sannan, ya shawarci ’yan uwansa iyayen yara, kan jajircewa wajen biyan hakkin makaranta ga wadannan Malamai da su ke dauke ma na nauyin mai girma na kokarin cusa ilimi da tarbiyya  ga ’ya’yanmu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: