Connect with us

NOMA

Published

on

Kafar sada zumunta ta zzmani da ake kira Selina Wamucii, an bude ta ne don taimaka yin hada-hadar, inda daga ko ina a fadin duniya za’a iya gudanar da hada-hadar sayen abinci da kuma fitar dashi zuwa kasar waje tare da sayen amfanin gona daga ko wacce kasa dake a cikin nahiyar Afirka.

Har ila yau, kafar ta kuma sanar da cewa, ta bude ne din amfanin manoma da kuma kungiyoyin kasuwanci, inda zasu dinga sayar da kayan su kai tsaye ga kasuwannin dake a fadin duniya.
Ta hanyar kafar ta Selina Wamucii, a dikin sauki tana taimakawa wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci daga ko ina a fadin duniya, tare da saye da kuma fitar da amfanin gona daga ko una a fadin nahiyar Afrika.
Bugu da kari, kafar ta Selina Wamucii, ta hanyar ta acikin sauki za’a iya biyan kudade kaya, tare da tabbatar da amincewa.
A yanzu haka, kafar ta Selina Wamucii, nayin maraba ga manoma, kungiyoyi masu zaman kansu, masu sarrafa amfanin gona da kuma kuniyoyin kasuwanci daga ko ina a fadin nahiyar Afrika.
Mai bukata zai iya shiga ta cikin wannan adiresin yanar gizo kamar haka: selinawamucii.com, inda zai fara sayar da kayan sa ko kuma amfanin gonar sa kai tsaye ga masu bukatar kayansa da suka fito daga fadin duniya.
Shugaban kafar Mista John Oroko, a cikin sanar da ya fitar, ya yi kira ga manoma suyi amfaninda kafar don sayar da amfanin gonakanbsu kai tsaye, ta hanyar yin rijista da kafar ta Selina Wamucii.
Shugaban kafar Mista John Oroko yaci gaba da cewa, kafar ta Selina Wamucii, ta kuma baiwa daukagin manoman da suka yi rijsita a da ita damar sanya ido kan amfanin gonarsa kai tsaye da ya tallata su a kasuwannin cikin gida da kuma kasuwannin dake a kasashen waje harda kasuwannin dake a nahiyar Afrika.
A cewar Shugaban na kafar ta Selina Wamucii, Mista John Oroko, saura irin abinda ake bukata daga gun manoman sune, yin rijsta da kafar yadda a cikin sauki, manomi shima zai zamo da a cikin kafar.
Shugaba Mista John Oroko ya kara da cewa, a kafar ta sadarwa ta Selina Wamucii, munyi amannar cewa, daukacin manoma da kuma masu sarrafa amfanin gona za’a iya sada su kai tsaye da kasuwannin dake a fadin duniya, musamman kasuwannin dake a fadin nahiyar Afrika.
Shugaban kafar Mista John Oroko ya sanar da da cewa, hakan ne ya bamu kwarin gwaiwar bude kafar ta zamani, musamman don amfanin manoman dake a fadin bahiyar Afrika.
A karshe, Shugaban na Selina Wamucii, John Oroko ya ce, kafar tana kuma yin amfani da fasahar zamani wajen samun bayanai da kuma tallata kayan amfanin gona a daukcin fadin nahiyar Afrika.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: