Connect with us

LABARAI

Boko Haram Ta Kashe Sojoji 70 A Sabon Harin Borno 

Published

on

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya habarto cewa wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun halaka sojoji Nijeriya su kimanin 70, a wani kwanton-baunan da su ka yi wa kwambar sojojin a jihar Borno da ke arewa maso gabas- kamar yadda majiyar sojojin ta tabbatar masa ranar Talata.

Bugu da kari kuma, maharan sun yi amfani da makamin roka a harin kwanton-baunar, inda su ka auna wata babbar motar da take dauke da sojojin a sa’ilin da take tsakiyar tafiya, kusa da kauyen Gorgi a jihar Borno a ranar Litinin, kamar yadda wasu sijoji biyu da basu amince a bayyana sonayen su ba su ka shaida wa kamfanin AFP.
“Wanda harin ya yi muni sosai, saboda ya jawo akalla sojoji 70 ne su ka halaka a wannan farmakin kwanton-baunar,” a ta bakin daya jami’in sojojin.
“Har wala yau kuma, kai tsaye wadannan yan ta’addan sun kitsa kai wa wannan motar ne wadda take cike da sojojin ta hanyar amfani da makaman RPG tare da tarwatsa motar inda suka halaka kusan duk sojojin da su ke ciki”. In ji jami’in sojojin na biyu.
“A halin da ake ciki yanzu, an kai ga zakulo gawawakin sojoji 70, amma akwai yuwuwar gano karin wasu, saboda yanzu haka aikin yana ci gaba da gudana”.
A hannu guda kuma, majiyar ta kara da cewa akwai karin wasu sojojin da su ka samu raunuka kana kuma mayakan sun yi awon gaba da wasu.
A gefe guda kuma, mai magana da yawun rundunar sojojin Nijeriya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP a halin yanzu ba zai ce komai ba dangane da labarin kai harin.
Haka zalika kuma, wannan ayarin sojojin ya tashi ne daga sansanin sojojin yanki da ke birnin Maiduguri, kan hanyar sa domin kaddamar da wani samame a wata tungar mayakan ISWAP da ke yankin tare da hadin gwiwar yan sa kai a jihar don yaki da yan ta’addan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: