Connect with us

MANYAN LABARAI

Coronavirus: Gwamnatin Bauchi Ta Kulle Kasuwannin Jihar

Published

on

Da Diminsa:

Coronavirus: Gwamnatin Bauchi Ta Kulle Kasuwannin Jihar

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnatin jihar Bauchi a yanzu-yanzu ta sanya dokar ta baci na rufe dukkanin kasuwannin da suke jihar domin kariya daga cutar Coronavirus.

Inda gwamnatin ta shaida cewar dokar za ta fara aiki ne daga gobe Alhamis.

Da yake ganawa da ‘yan jarida a gidan gwamnatin Bauchi daidai karfe 5:20pm, mataimakin gwamnan jihar, Sanata Baba Tela ya shaida cewar daukar matakin ya zama dole domin kariyan kai daga cutar ta Coronavirus.

A bisa haka ya ce gwamnan jihar Bala Muhammad ya umurci ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su tursasa wa ‘yan kasuwa bin wannan umurnin.

Sai dai mataimakin gwamnan ya shaida cewar umurnin rufe Kasuwannin bai shafi masu saida kayyakin abinci, magunguna da gidaje saida Mai na fetur hadi da manyan shaguna (Super market) ba; inda ya ce kawo yanzu wadannan rukunin masu sana’ar ne kawai aka lamunce su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancinsu kafin zuwa mataki na gaba.

Daga gobe Alhamis masu saida maguna, da kayan abinci, da gidajen mai tare da manyan shagunan saida kayyaki ne kawai gwamnatin ya amince su ci gaba da saida kayyakinsu.

Sai dai mataimakin gwamnan ya shaida cewar za su bude Kasuwannin daga lokacin da cutar ta kawo karshe.

Cikakken wannan labarin na tafe daga baya:
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: