Connect with us

RIGAR 'YANCI

Covid-19: Nijeriya Ta Haramta Shigowar Bakin Haure Da Bada Fasfo

Published

on

Sakamakon barkewar cutar sarkewar numfashi da aka yi wa lakabi da Covid-19 a fadin duniya, akwai bukatar mayar da hankali sosai a kan yadda za a shawo kanta bisa la’akari da irin barnar da take wa koshin lafiyar dan Adam a doron kasa.

Domin bayar da gudunmawa ga shawo kan cutar a Nijeriya, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS) Muhammad Babandede ya umurci a dakatar da aikin bayar da fasfo da yi wa baki ‘yan kasar waje da ke zama a Nijeriya rajista na wucin-gadi, daga ranar 23 ga watan Maris zuwa 23 ga Afirilun 2020, kamar dai yadda yake kunshe a umurnin da gwamnatin tarayya ta bayar na rufe sashen sufurin jiragen sama na kasashen waje.
A halin da ake ciki kuma, sanarwar da Jami’in yada labaran NIS, DCI Sunday James ya fitar ga manema labarai ta yi bayanin cewa Hukumar ta NIS za ta yi amfani da damar dakatar da aikin fasfon wajen kammala wadanda aka riga aka fara aikinsu kuma za a sanar da jama’a da zarar an kammala domin karba.
Hukumar ta ce ta ji takaicin irin yanayin da al’umma za ta tsinci kanta a ciki a wannan lokacin sakamakon matakin da ta dauka, kana ta tabbatar wa da ‘Yan Nijeriya ci gaba da gudanar da aikinta kamar yadda ya kamata.
Bugu da kari, ta bayar da lambobin wayar da za a iya tuntubarta idan bukatar gaggawa ta taso kamar haka: 07080607900, 08119753844, 08147199908.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: