Connect with us

RIGAR 'YANCI

Covid-19: Sai Na Kare Jihar Yobe Ko Ta Halin kaka – Gwamna Buni

Published

on

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar ingantattun matakan dakile yaduwar hattsabibiyar cutar nan ta numfashi ta ‘Corona-birus’ don kare rayukan jama’ar jihar Yobe, musaman ganin yadda gwamnatin jihar ta fara da daukar matakin kafa cibiyar kebance wadanda ake tsammanin sun harbu da ita, tare da kawo kayan aikin da ake bukata.

Gwamnan ya furta hakan a wata sanarwar manema labarai wadda ta fito daga ofishin babban Daraktan sa na yada labarai da hulda da gidajen jaridu- Alhaji Mamman Mohammed inda ya kara da cewa, haka kuma gwamnan ya bayar da umurni ga kwamishinan ma’aikatar kiwon lafiya kan su kasance cikin ko-ta-kwana, wajen daukar ingantattun matakan yaki da cutar.
Alhaji Mamman ya ce, Gwamna Buni ya nanata cewa gwamnatin sa za ta bayar da cikakken goyon baya tare da hadin kai a dukan matakan yaki da cutar don dakileta a fadin jihar.
Ya ce, Gwamnan ya bukaci goyon bayan ilahirin al’ummar jihar Yobe wajen bayar da rahoton duk wani da ake zargin kamuwa da cutar cikin gaggawa don daukar matakin da ya dace a likitance.
Sannan kuma ya yi kira ga jama’ar jihar da su ci gaba da amfani da shawarwarin da kwararrun masana a fannin kiwon lafiya su ke bayar wa tare da lizimtar tsabtar jiki da muhalli ta hanyar wanke hannu a kai a kai.
A gefe guda kuma, Gwamna Buni ya bayar da umurnin aiwatar da matakin wayar da kan jama’a kan cutar Covid-19 a kowane lungu da sakon jihar Yobe.
Daraktan yada labaran ya kara da cewa, Gwamna Buni ya tunatar da al’ummar jihar a kasancewar su masu rike da addini sau-da-kafa da cewa su guji yada zantuka maras amfani kan cutar, ya ce su ci gaba da addu’ar neman mafita daga Allah kan wannan ibtila’in da ake ciki.
“Mu ci gaba da mika lamarin mu zuwa ga Allah tare da lizimtar addu’o’in neman taimakon Allah, don ganin bayan wannan kalubalen da ya fuskanto mu”. In ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: