Connect with us

MANYAN LABARAI

Covid-19: Yadda Kyari Ya Kamu A Hidimar kasa

Published

on

  • Bai Harbi Buhari Ba
  • Ma’aikatansa Uku Sun Kamu
  • Da Su Wa Kyari Yi Mu’amula?

 

A jiya Talata, 24 ga Maris, 2020, rahotanni su ka tabbatar da cewa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Nijeriya, Malam Abba Kyari, ya kamu da muguwar cutar nan ta Covid-19, wacce a ka fi kira da Coronavirus biyo bayan wata tafiyar da ya yi zuwa kasar Jamus, don aikin hiidimar kasa, kasar da kowa ya san yadda annobar cutar ta mamaye ta, inda a ka tabbatar da cewa mutane fiye da 30,000 sun kamu da Covid-19 din a Jamus.
Kyari ya je kasar ne a kokarinsa na tattaunawa da kamfanin Siemens AG, don gyara hasken wutar lantarkin Nijeriya, wacce a ka dade a na fama da matsalarta.
Rahotanni sun nuna cewa, bayan dawowarsa da ’yan kwanaki ya fara tari a wajen zaman Kwamitin Fadar Shugaban kasa kan dakile annobar ta Covid-19, inda nan take a ka shawarce shi da ya je a duba lafiyarsa.
Dattijon dan shekara fiye da 70 a duniya, bai yi taurin kai kuwa ba, inda ya je a kashin kansa a ka gwada shi, kuma a ka tabbatar da cewa, ya na dauke da cutar. Hakan ya bayar da damar fara kula da lafiyarsa tare da daukar matakan da su ka dace.
A cikin matakan da a ka dauka har da yi gwaji ga dukkan mutanen da a ka san ya yi mu’amula da su ta kurkusa tun bayan dawowarsa daga kasar ta Jamus, ciki kuwa har da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, wanda sakamakon gwajin ya nuna cewa, ba ya dauke da cutar.
To, amma bayanai sun nuna cewa, uku daga cikin ma’aikatan Abba Kyarin su na dauke da cutar. Sai dai kuma ba a bayyana sunayensu ba.
Kyari, wanda a kan hanyarsa ta dawowa daga Jamus ya biya ta kasar Masar, don cigaba da tattaunawa kan ayyukan kasa, yanzu a na sa ran za a dauke shi zuwa birnin Ikko, domin ba shi kulawar da ta fi dacewa. Ita ma dai Masar (wato Egypt) ta na cikin kasashen Afrika da su ka fi fama da cutar ta Covid-19.
Cutar dai ta fara bulla ne a kasar Sin a garin Wuhan karshen watan Disamban 2019, amma yanzu ta yadu zuwa kasashe akalla 169, ta kashe 18,200, yayin da 409,000 ke fama da ita zuwa yanzu. Wannan ya faru ne sakamakon yadda cutar ke saurin yaduwa ta hanyar mu’amula.
A cikin mutanen da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Nijeriyan ya yi mu’amula da su akwai Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya je yi ma sa ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa, ministoci da dama, kamar na yada labarai, ayyukan musamman, karamar Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja da na harkokin kasashen waje.
Bugu da kari, akwai Kakakin Shugaban kasa Garba Shehu da makamantansu. Sannan akwai Babban Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya, Sakataren Gwamnatin Tarayya da wasu da dama.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: