Connect with us

RIGAR 'YANCI

Covid-19: Yobe Ta Umurci kananan Ma’aikata Su Gudanar Da Ayyuka Daga Gida

Published

on

A kokarinta daukar matakan dakile yaduwar cutar ‘Corona-birus’ jihar Yobe, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin wayar da kan jama’a a karkashin mataimakin gwamna, Alhaji Idi Barde Gubana, inda kuma ya ayyana wasu matakai da su ka kunshi murtar kananan ma’aikata a jihar- daga mataki na 12 zuwa kasa, da cewa su zauna gida, kar su fita aiki, kana su gudanar da ayyukan su daga can.

Jim kadan da kaddamar da kwamitin, yau Talata (jiya) ya fitar da sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishina a ma’aikatar yada labarai, harkokin yau da kullum da al’adu, Alhaji Abdullahi Bego, tare da shaidar da cewa, a kokarin sa wajen dakile barkewar annobar Covid-19, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya bayar da umurnin kafa kwamitin are da mika akalar sa ga mataimakin sa, Hon. Idi Barde Gubana.
Ya ce kwamitin ya kunshi kwamishina a ma’aikatar kiwon lafiya, ta yada labarai, ta bayar da agajin gaggawa da abkuwar ibtila’i, ta kasuwanci, ta mata, ta zirga-zirga da makamashi, ta muhalli, matasa da wasanni, addinai hadi da shugaban majalisar sarakunan jihar, kwamishinan yan-sanda, Daraktan yan-sandan ciki, kwamandan jami’an tsaron al’umma.
Sauran sun kunshi majalisar dokoki, asibitin koyarwar jami’ar jihar Yobe, hukumar kula da asibitocin jihar, hukumar SEMA, WHO da makamantansu.
Bugu da kari kuma, biyo bayan taron da kwamitin ya gudanar, ya cimma matsaya wajen daukar matakan kariya da dakile yaduwar cutar kamar haka.
Dukan kananan ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa su dakata daga zuwa wajen aiki, kana su zauna gida tare da gudanar da ayyukan su daga gida. Amma matakin bai shafi ma’aikatan musamman ba, irin ma’aikatan kiwon lafiya, ruwan sha da na SEMA, yan jaridu tare da na ma’aikatar kashe gobara.
Haka kuma, kwamitin ya bukaci jama’ar jihar, daga yanzu su ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum ta hanyar yin nesa da nesa da juna, lizimtar tsabta ta hanyar wanke hannu lokaci bayan lokaci da ruwan sabulu. Kana su rika amfani da kyalle ko makamantan su don rufe baki da hanci da kiyaye tari ko atishawa cikin jama’a.
A hannu guda kuma, kwamitin ya bukaci jama’a su takaita gudanar da tarukan kowadane iri ne. Kana da bayar da shawara dangane da jama’ar da ke shigowa daga wasu bangarorin da aka tabbatar da bullar cutar Covid-19 da cewa su duba girman Allah, su killace kansu daga cudanya da jama’a tsawon kwanaki 14.
Kwamitin ya yi kira ga jama’a da shugabanin wuraren ibada da tashoshin mota da sauran su, da cewa su samar da kayan wanke hannu, a duk lokacin da mutane su ka zo shiga wuraren.
Haka kuma, kwamitin ya bayar da shawarwari daban-daban don kaucewa barkewar cutar, kana da bayar da lambobin wayar tafi-da-gidanka: 08131834764 da 07041116027, don tuntuba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: