Connect with us

RIGAR 'YANCI

Cutar Covid-19 Ta Tsayar Da Komi A Duniya – Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Published

on

Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya, Mista Antonio Guterres, ya yi kira ga al’umman Duniya da su mike tsaye domin taimaka wa wadanda cutar Koronabairos ta rutsa da su.

Ya ce wannan mummunar cutar da ta bullo cikin wannan shekarar ta yi illa ga dubbannin al’umma. Ya ce; cutar ta Numfashi tana shiga kasashe dabam-dabam.
Ya ce ya zama wajibi mu mike tsaye domin magance cutar da ke yaduwa cikin sauri. Ya ce; kowa abin ya shafe shi dole ne mu taimaka ma wadanda cutar ya shafa saboda idan suka kasance tare da cutar za ta iya shafan kowa.
Ya ce; cutar Koronabairos ta yi illa ga mata da yara da tsofaffi, kuma tana kara yaduwa zuwa wasu kasashe.
Ya ce; wannan annobar ba ta bar kowa ba, tana kisa tana addabar al’umma.
Ya yi kira ga kasashen Duniya da su hada kai domin kariya daga al’ummun su. Sannan ya bukaci al’umma da su kasance masu tsaftace hannaye da sassan jiki da muhalli saboda cututtuka.
Ya kuma roki masu hannu da shuni da su taimaka wa nahiyar su, domin ceto rayuwar masu cutar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: