Connect with us

KANNYWOOD

Mun Samar Wa Jaruman Kannywood Cigaba – Alhassan Kwalle

Published

on
A daidai lokacin da ya rage kasa da mako daya a gudanar da zaben shugabancin kungiyar Jaruman Kannywood ta kasa, wacce JARUMI ALHASSAN KWALLE ya ke jagoranta har zuwa wannan lokacin babu wani dan takara da ya fito wanda zai kara da shi Alhassan Kwalle din a takarar. Baya ga haka kuma shi kansa tsarin gudanar da zaben ya zo da wani sabon salo ta yadda za a gudanar da zabe ba tare da an rushe shugabancin ba, kuma ba tare da kafa kwamitin zabe ba. Kan haka ne LEADERSHIP A YAU ta nemi jin ta bakin Alhassan Kwalle dangane da irin wannan sabon salo, sannan kuma a gefe guda ya yi ma na bayani kan irin cigaban da su ka samar a lokacin shugabancin nasu. Ku biyo mu ku ji yadda hirar ta kasance:

Ka samu tsawon lokaci a kan shugabancin kungiyar jarumai, kuma a yanzu nan da sati za a gudanar da sabon zabe. Ko me ya ba ka kwarin gwiwar fitowa neman zango na biyu a maimakon ka bar wa na baya?
Alhassan Kwalle: To ka san har kullum shi shugabanci dama ba ka yin sa sia kana da manufa, kuma ko da rikon kwarya  za a ba ka sai an fahimci ya ya kake wacce manufa kake da ita da za ta ciyar da al’ummar da kake shugabanta gaba? To daman mu manufar mu ba ta wuce kamar guda uku ba. A samu kyakkyawan hadin kai a masana’antar da girmama na gaba, sai kuma samar da abubuwa na ci gaba. To wadannan abubuwa sune dai suka sa muka shigo wannan harka. Kuma daidai gwargwado muna ganin mun kwatanta abinda mutane suke ganin ya yi musu daidai. Shi ya sa da aka zo wannan zabe gaskiya na so na hakura saboda kalubalen da ake fuskanta daga wasu daga cikin ‘yan wannan masana’antar. Suka ce sai dai ni na sake tsayawa. To irin wannan ya sa na ga tun da odn al’umma nake yi kuma suka nemi da na kara tsayawa, don haka muka hakura muka kara tsayawa, don ba mu san abin da Allah zai yi ba nan gaba.

To shi wannan yanayi na zaben ya bambanta da zabukan da aka gudanar na kungiyoyi ta yadda a ke rushe shugabanci a kafa kwamitin zabe, amma shi wannan zaben da aka tsara ba a yi hakan ba.
To, haka ne, amma dai abin da mu mu ka lura da shi hakan da aka yi bai karya tsarin mulkin kungiyar mu ba, kuma yin hakan ya fi maslaha don haka domin mu saukaka wasu abubuwa sai muka tafi a kan wannan tsairn, kuma hakan zai baiwa kowa damar ya fito ya nemi mukamin da yake so. Kuma ko da wancan din muka yi wasu dai za su koma gefe ne suna fadar maganganu kuma ko ba komai za ka ga shi wannan tsarin haka aka sunnata shi a kasar nan, shugaba yana kai ake gudanar da zabe, don haka ba mu muka fara ba, kuma masu shirya zaben cin gashin kansu suke yi babu wani katsalandan da za mu yi musu a cikin aikinsu don kwararru ne a kan harkoki na duniya.

An san ba za ka rasa samun adawa ta cikin gida ba, ba ka ganin yin hakan zai sa wasu su rinka ganin ka mamaye komai shi ya sa ba su fita ba?
To ai babu maganar an mamaye komai tunda abu na amana da jama’a suka dora maka kada yake wasu daga gefe sun yi ta zama a warware daban da ban don kokarinsu na ganin an canza ni, to amma da yake masu bukatar na ci gaba sun fi yawa ka ga hakan bai sa sun yi nasara ba, domin su a wajen su abin da suke ganin babban laifina, shi ne mun hada kai da gwamnati, to mu a matsayinmu na ‘yan kasa kuma ‘yan jihar Kano, dole ne mu hada kai da gwamnati, domin samar da ci gaba a masana’antar mu sai kuma maimakon su fito a yi takarar da su sai kuma ba su fito ba wannan ya nuna cewar mun fi su kishin masana’antar shi ya sa mutane suka sake nemo mu domin mu ci gaba kuma muna rokon Allah ya ba mu nasara a kan abinda muka sa a gaba.

To wai me ma Alhassan Kwalle ya yi a shugabancin sa da har ake bukatar ya kara ci gaba?
E to, ina ganin su mutanen da suke so na ci gaba sune za su iya bayar da wannan amsar, amma dai abinda na sani shi ne kusan shekara hudu baya lokacin da aka rantsar da shugaban Hukumar Tace Finafinai, Isma’ila Afakallahu, ya kirawo mu domin mu hadu kan mu yi shugabanci wanda kafin lokacin babu, to kuma sia aka fito da tsarin cewar ya kamata kowacce kungiya ta san yawan ‘ya’yanta yadda za zama an yi wa abin katanga babu wanda zia hauro sai dai ya shigo ta kofa, amma aka shafe shekara hudu babu wanda ya yi sai kungiyar masu tace fim amma duk sauran babu wanda ya yi sai ya zama mun samu kan mu a cikin wani yanayi, mutane sun shiga cikin masana’antar an cika ta babu tsari ba dokoki, babu tsawatarwa. To shi ne da Afakallahu ya dawo karo na biyu sai ya gayyace mu don mu zo a yi amfani da karfin gwamnati don a gyara harkar. To sai ya zama mune na farko domin duk abinda aka ce gyara ta kungiyar jarumai, mune a kan gaba. Don haka muka had akai da Gamnati don a kawo gyara. Kuma wannan gyaran duk cikin Kannywood babu wanda ya amsa kamar kungiyarmu. A kan haka mun cimma nasarorin da a baya sun fi karfinmu, ba don haka ba ba da ba mu samu damar yin ayyukan da mutane za su gani su ce suna bukatar mu kara ci gaba ba, domin a sakamakon haka mun yi wa kungiyar rajista wanda a baya duk zaman da ake yi kungiyar ba ta da rajista kuma dalilin hadin kan da muke bai wa hukumar tace finafinai ya sa kungiyar ta samo office wanda a baya babu, amma a yanzu jarumai suna da ofishin kugiya duk wand aya tashi nan zai zo ya gudanar da jarkokinsa a matsyainsa na dan kungiya, kuma a yanzu kwa ya yarda da cewar kungiyar za ta tsaya masa don haka mu kuma komai  dare idan wani abu ya samu dan kungiya mukan yi kokarin mu ga mun samar masa da mafita, kuma a kan wannan hadin kan ya sa muka samu kyakkyawar fahimta ga Hukumar ‘Yan sanda ta Jihar Kano wanda mu ka kai musu ziyara tare da gabatar musu da manufofinmu. Sannan ya sanar da jami’ansa cewar duk wani abu da ya taso na ‘yan fim kafin DPO ya dauki mataki ya mayar da shi zuwa kungiya. Idan ya fi karfinta sai su yi nasu. To hakan ba karamar nasara muke samu ba. Wannan ya sa su ma ‘yan kungiyar su ke ba mu hadin kai fiye da lokutan baya.

Daga karshe wane kira za ka yi ga ‘yan kungiyarka?
To ni babu abinda zan ce illa dai na yi kira ga mu shugabanni da lokacin mu ya kare mu ke neman komawa da kuma wadanda su ke nema a yanzu, to ya kamata mu sani cewar, kungiya ce da sai dai ka zo ka bautawa ‘ya’yanta. Ba kungiyoya ba ce da za ka zo ka saka ta a aljihu ko ka nemi kudi da ita ba. Don haka na yi alkawarin in dai ina raye kamar yadda na yi wa kungiyar nan rajista, zan tsaya na ga wasu ba su zo sun yi amfani da ita ba don biyan bukatar kansu. Don haka kungiyar mu ba ta rigima da gwamnati ba ce, kuma ba za mu yarda wani ya zo ya siyasantar mana da kungiya ba.

To madalla, mun gode.
Ni ma na gode.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: