Connect with us

KIWON LAFIYA

Rigakafin BCG Ba Ta Hana Kamuwa Da Tarinfuka, Cewar Masana

Published

on

Ko mutum ya samu allurar rigakafi ta cutar Tarinfuka (TB) wadda ake yi lokacin mutum yana yaro, wannan ita kadai ba zata iya kare mutum dag akamuwa da cuttar ba. Kamar dai yadda wani kwararre ta bangaren kiwon lafiya Odume Betrand ya bayyana.

Bacilli Calmette-Guerin (BCG) ita dai allurar rigakafin kamuwa da cutar Tarinfuka ce, sau da yawa kuma ana yi ma Jarirai ne lokacin da aka haife su. Ko dai akwai wani labarin da yake nuna su mutanen da aka yi ma allurar ta rigakafin sun kuma kamu da cutar.
Wannan ma shine ya yi bayanin dalilan da suka sa ana samun su matsalolin Tarinfuka, har madaga cikin kananan yara, ko kuma mutanen da aka yi masu allurar rigakafin ta BCG suna kananan yara ko kuma bayan an haife su.
Mista Betrand wani babban jami’i ne kwararre kuma mai tsare- tsare akan cututtukan da suka shafi Tarinfuka da kuma kanjamau, a cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka, ya bayyana cewar ita allurar ta rigakafi tana rage tsananin ita cutar ne kawai, idan har an kamu da ita, saboda wasu mutane tuni suna tare da cutar ta Tarinfuka. latent TB. Latent TB dai wani nau’i ne na cutar Tarinfuka wanda shi kuma lokacin da mutum yake dauke da kwayoyin cuta, suna da kwayar cutar jikinsu sai dai kuma, amma kuma basu da yawa. Wannan kuma yana kasancewa haka ne saboda su kwayoyin halitta wadanda ke jikin mutum, sune suke dakushe su, saboda dama suna can wurin ne saboda su hana kwayar cuta samun dama cutarwa ta hanyar data shiga jikin mutum. Wadanda suke dauke da irin wannan cutar ta Tarinfuka basu jin ciwon ita cutar,ba kuma za su watsa su kwayoyin cutar ba, koda kuma an duba kirjinsu ba za a iya ganin komai ba. Amma kuma a hankali zata iya rikidewa ta koma Tarinfukar na ainihi.
Ya bayyana cewar idan har mutum yana tari wanda har ya kai fiye da mako biyu, dole ne ayi tsammanin an kamu da ita cutar ta Tarinfuka, ya kuma kamata ya je a ayi mashi gwaji. Shi kuma gwajin ana yin shi kyauta ne a asibitocin gwamnati.
“Sa kudade wajen yin bincike”
kwararren ya bayyana hakan ne lokacin jajibirin ranar Tarinfuka ta duniya wanda aka yi a Abuja ranar Alhamis ta makon daya gabata. Ya tunatar da mutane cewar ita sabuwar cutar ta Tarinfuka, wadda kuma ana iya maganinta ne, amma sai an dauki mataki da wuri, sai kuma idan mutane sun bayyana halin da suke ciki.
Ya nuna rashin jin dadin shi ganin yadda ita cutar yanzu ta kasance ita ce ta daya a kasar Nijeriya, a matsayin cuta wadda take addabar mutane. Wato kasashen da suka da matsalar ita cutar, wadanda kum,a har zuwa yanzu suna magane akan, ma yadda za su iya gano ita cutar, da kuma maganinta. Yayin da su kuma kasashen da suka ci gaba, su maganar yadda za su ma yana kamuwa da ita da kuma yaduwar ta gaba daya.
“Idan an yi ma mutum ita allurar tak rigakafi lokacin yana yaro, hakan ba zai iya kare ko kuma hana mutum daga kamuwa da cutar ba, babban aikin da take yi shine ta rage kaifin ita cutar, amma kuma shi abin ba zai kasance na irin mutanen da basu samu yin allurar ta rigakafin ba”.
Ya cigaba da yin karin haske dangane da ita cutar saboda ita cutar ana iya kawo karshen yadda take addabar mutane da kuma yaduwarta a duniya, kamar dai yadda shi Mista Betrand ya kara bayanin akwai wasu abubuwan da ake bukata a samu cimmawa, kamar shi al’amarindaya shafi allurar ta rigakafi da kuma maganin ita cutar gaba daya.
“Ba zamu yi maganar kawo karshen ita cutar ta Tarinfuka ba, ba tare da wata allura ba, ya kamata mu rika yin magana akan yadda za asa kudade wajen yin bincike dangane da ita allurar. Akwai bincike- bincike masu yawa da ake gudanar da su domin cutar ta Tarinfuka, amma kuma wani al’amari daban shine har zuwa yanzu ba daya daga cikinsu wanda aka amince dasu.”
Tarinfuka cuta ce wadda tafin saurin yaduwa a duniya da kuma babban hadari wajen kashe al’umma.
Ko wacce rana kusan mutane 4500 suke rasa rayuwarsu a sanadiyar ita cutar ta Tarinfuka, bugu da kari kuma kusan mutane 30,000 sun kasance ne cikin cutar da ake iya maganin ta da kuma hanata yaduwa.
Babban jami’i kuma kwararre na bangaren Tarinfuka Ayodele Awe, ya bayyanna cewar, da akwai bukatar a kara wayar da kan al’umma,dangane da cutar Tarinfuka a Nijeriya, wannan kuma zai kasance hakan ne saboda a gano shi bakin tsaren.
Ya yi karin haske inda yace idan har ana bukatar a samu cimma shi wannan burin kamar yadda ya kamata, banagrean watsa labarai suna da gaggarumar gudunmawar da zasu bayar wajen gamawa da cutar ta a Nijeriya.
“Muna bukatar shi bangaren watsa labarai su tashi wajen yin abubuwan da suk dace, wajen wayar da kan al’umma, akan ita cutar ta Tarinfuka a Nijeriya. Yawancin mutane basu ma san ko kuma gane su alamun na cutar ba, wannan ma shi kanshi abin yana shafar nasu kokarain da suke yin a sanin yadda za su kubutad da kansu daga kamuwa da cutar.
“Ita cutar TB ana iya gane ta, maganin ta, da kuma kawar da ita daga doron kasa, amma shi kuma ko ita matsalar cutar a Nijeriya, akwai wasu abubuwan da har yanzun ba asan dasu ba,wadanda kuma zasu kasance tamkar wata manuniya ce na yadda cutar take kara yaduwa.
“Ko wacce cutar Tarinfukar da ba iya ganowa ban a iya kasancewa matsala ga mutane 10 zuwa 15, cutar tana samar da matsalolin rashin lafiya ga kusan mutane miliyan 10 ko wacce shekara.
“Muna yin wannan aikin lokaci mai tsawo, ni kuma na fara yin aikin daya shafi Tarinfuka shekara 30 da suka wuce, amma kuma ko wanne lokaci duk rahoto daya ne ake samu babu wani canji. Ya kamata mu duba da gano mutane 400,000 ko wacce shekara, amma kuma 100,000, ne muke yi, wannan kuma ya nua ke nan muna rasa 300,000 wau matsalolin da suke samar da cututtuka daban -daban , a sanadiyar ita cutar
Ya yi karin haske inda yace idan har ana bukatar a samu cimma shi wannan burin kamar yadda ya kamata, banagrean watsa labarai suna da gaggarumar gudunmawar da zasu bayar, wajen gamawa da cutar ta a Nijeriya.
“Mu na bukatar shi bangaren watsa labarai su tashi wajen yin abubuwan da suk dace, wajen wayar da kan al’umma, akan ita cutar ta Tarinfuka a Nijeriya. Yawancin mutane basu ma san ko kuma gane su alamun na cutar ba, wannan ma shi kanshi abin yana shafar nasu kokarain da suke yin a sanin yadda za su kubutad da kansu daga kamuwa da cutar.
“Ita cutar TB ana iya gane ta, maganin ta, da kuma kawar da ita daga doron kasa, amma shi kuma ko ita matsalar cutar a Nijeriya, akwai wasu abubuwan da har yanzun ba asan dasu ba,wadanda kuma zasu kasance tamkar wata manuniya ce na yadda cutar take kara yaduwa.
“Ko wacce cutar Tarinfukar da ba iya ganowa ban a iya kasancewa matsala ga mutane 10 zuwa 15, cutar tana samar da matsalolin rashin lafiya ga kusan mutane miliyan 10 ko wacce shekara.
“Mu na yin wannan aikin lokaci mai tsawo, ni kuma na fara yin aikin daya shafi Tarinfuka shekara 30 da suka wuce, amma kuma ko wanne lokaci duk rahoto daya ne ake samu babu wani canji. Ya kamata mu duba da gano mutane 400,000 ko wacce shekara,amma kuma 100,000, ne muke yi, wannan kuma ya nuna kenan mu na rasa 300,000 wau matsalolin da suke samar da cututtuka daban-daban a sanadiyar ita ce.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: