Connect with us

TATTAUNAWA

Tafarnuwa Na Maganin Cutar Coronavirus – Malam Maikudi

Published

on

Tun daga lokacin da cutar da ta addabi duniya a yau ta Cobid-19, wato Coronavirus, masana maganin Bature da kuma masana maganin da ke da jibi da Musulunci, sun tashi tsaye na ganin sun bayar da gudunmuwarsu, domin yi wa wannan cuta kamun kazar-kuku. Kan haka, wakilin LEADERSHIP A YAU, ISA ABDULLAHI GIDAN bAKKO, ya sami damar zantawa da wani fitaccen malamin addinin Musulunci kuma masanin maganin da su ke da alaka da addinin Musulunci mai suna MALAM MUHAMMADU ABUBAKAR, wanda a ka fi sani da MALAM MAIKUdI da ke Hayin Dogo a  Samaru cikin karamar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna.

Malamin ya amsa tambayoyin wakilinmu kan dalilansa na tabbatar da cewar, tafarnuwa na maganin cutar ta Coronavirus. Ga yadda hirar ta kasance:

A kwai wani bincike da ka yi kan maganin da ka ked a tabbacin zai dakile rayuwar wannan cuta a jikin dan adam?
Lallai na yi bincike a kan wannan cuta ta Coronavirus kuma daga binciken da na yi, na fahimci ta na da tarihi, ta na kuma tarihi, na kuma fahimci daga inda ta ke ya zuwa ga dan adamu. Na fahimci ta na shiga jikin mutum ta hanyoyi kamar haka, ma fi sauri shi ne ta iska,saboda cutar ta da alaka na kusa da iska, na kuma fahimci ta na da saurin tafiya, tamkar hayaki.

An fi daukar cutar ta wanda ya kamu ko kuma in mai dauke da cutar ya ci abinci ya rage, mjutum ya ci sauran abincin, shi ma zai kamu kenan?
Baya ga dukkanin abubuwan da ka bayyana, kazanta da barin hannu a cikin kazanta ba tare da wanke hannu ba, kuma cin abinci da wanda ke dauke da cutar, shi ma matsala ne, domin in dai har ya na numfashi, kai da ba ka da cutar, za ka dauka a cikin dan kankanin lokaci, ko da ma bayan mai dauke da cutar ya ci abinci a kwano, ba a wanke ba, ka dauka ka ci, kai ma za ka kamu da cutar. Sauran hanyoyin sun hada da in ya yi attishawa kusa da kai za ka iya daukar cutar, maganin ta kawai ka nisanta kan ka nesa daga wanda a ka ga alamun cutar tare da shi, da kuma nisanta yin mu’amala da duk wani abu da mai cutar ya yi amfani da shi, bincike ya tabbatar da cewar, a cikin mintuna goma za ta iya kama mutum ashirin, in dai mutum zai shaki iska, to ya na tare da hadarin kamuwa da wannan cuta.

Mene ne alamun ta bisa binciken da ka yi?
Alamun cutar ta Coronavirus su na da yawa, amma ma fi saukin ganewa su ne zafin jiki da ciwon kai da zazzabi kyarmar jiki da shakewar murya da zafin kirji, sannan mutum ya ji kamar a kwai yaji a cikin kirjinsa, sai mutum ya ji numfashinsa na fita kyar, tamkar mai cutar asma.

Ya butun toshe baki da hanci da jama’a ke yi a lokutan iska ko sanyi ko kuma lokacin da kura ke yawan motsawa?
Babu ko shakka toshe hanci da kuma nizanta da juna, wato tsakanin mutum da mutum a sami tazara mai nisa, za su tallafa wa wadanda ba su kamu da cutar ba, su sami kariya da kuma da zarar an sami alamun wani ya kamu da cutar, a nisanci mu’amala da shi, wannan ma mataki ne mai muhimmanci da al’umma za su dauka.

A bisa binciken da ka gudanar, ka gano wani abu da zai iya zama magani ko kuma kariya ga al’umma daga daukar wannan cuta ta Coronavirus?
Babu shakka na gudanar da bincike, kuma na gano Tafarnuwa za ta yi maganin wannan cuta da ta ke addabar al’umma a sassan duniya a yau, kuma kafin ma in gano wannan magani babu wanda ya san yawan muhimmancin Tafarnuwa a jikin dan Adam,a yau ko da mura ce ta addabi mutum, in har ka hadiye Tafarnuwa, murar za ta bace baki daya a cikin dan kananin lokaci, sauran amfanin Tafarnuwa sun hada da maganin Asma da yadda wasu za ka ga su na da kiba, da zarar sun fara hadiyar Tafarnuwa za ka sun sabe a lokacin da bai da tsawo.

To, mutum zai kwaba Tafarnuwan ne ko jikawa zai yi ko kuma hadiye wa zai yi daga lokaci zuwa lokaci?
Da farko in mutum ya sami kwarar Tafarnuwar, barata zai yi, zai ga yadda ta ke, sai ya dauki daya da safe da rana ma daya da kuma dare daya, in Allah ya yadda mutum ba zai kamu da wannan cuta ba, in ma mutum na tare da mura, zai rabu da ita, hasali ma dai, ita Tafarnuwa kariya ce daga ko wace irn cuta da ta ke jikin mutum, musamman da ya ke mafiya yawan cututtukan da su ka shafi sanyi, kamar wannan cuta da ta damu kowa a duniya a yau sanyi ne kuma a kirji ta ke.

A yau likitoci da kuma gwanatoci, ba su maganar Tafarnuwa a cikin maganar matakan kariya daga wannan cuta, me za ka ce a kan wannan batu?
To, ai shi rashin sanin abu ai ba bakon abu ba ne, su na magana ne a kana bin da suka sani, mu kuma mu na magana ne a kana bin da Allah Ya sanar da mu a Alkur’ani da kuma Hadisai da kuma haduwar malamai, duk wadannan batutuwa da su ke yi ai su ma bayanin abin da suka sani su ke furtawa, fata da shi ne Allah ya kawo mafitar da ake bukata.Kuma da za a samu wadanda aka same su sun kamu da wannan cuta, in har aka sami Tafarnuwa aka kona, su ka shaki hayakin, in Allah ya so za ka ga mutum ya sami sauki kuma in sha Allahu ya warke.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: