Connect with us

MANYAN LABARAI

Wane Hali Gwamna Bala Ke Ciki Bayan Ya Kamu Da Cutar Covid-19?

Published

on

A jiya da yammaci ne hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasar Nijeriya (NCDC) ta fitar da sakamakon gwaje-gwaje da ta yi wa mutum shida da ta ke zargin su na dauke da cutar Covid-19, wacce a ke kira da Coronabirus, a jihar Bauchi, inda ta tabbatar da cewar mutum daya daga jihar na dauke da cutar a yayin da mutum biyar daga cikinsu su ka kasance ba su dauke da cutar.
Hukumar ta ce, wanda ya ke dauke da cutar daga cikin mutune shidan da ta yi wa gwaji a kansu shi ne Gwamnan Jihar Bala Muhammad Abdulkadir, wanda ya ziyarci kasar Jamus a kwanakin baya tare da yin mu’amala da dan tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, wato Muhammad Atiku, wanda a ka tabbatar ya na dauke da cutar a tsakanin Legas zuwa Abuja kwanakin baya.
A cikin wata kwafin sanarwar manema labarai da babban mai taimaka wa Gwamna Jihar Bauchi shawara kan hulda da ‘yan jarida, Muktar Gidado, wanda ya fitar a jiya da yamman, ya shaida cewar gwamnan ya na cigaba da kasancewa a killace tun kafin fitowar sakamakon gwajin nasa, inda ya ce, zai kuma cigaba da kasance a killace har zuwa lokacin da zai samu lafiya daga cutar.
Ya kuma bayyana cewar, gwamnan ba ya cikin wani mummunan yanayi, domin kuwa har yanzu babu alamar galabaita a tare da shi, inda ya ce, ya na karkashin cikakkiyar kulawar likitoci.
LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewar, a shekaran jiya ne dai fadar gwamantin jihar Bauchi ta sanar da duniya cewar gwamnan jihar ya na killace, inda a ka debi jininsa, domin gwaji, saboda a gano ko ya na dauke da cutar ko babu biyo bayan mu’amala da musabaha ta musamman da su ka yi da dan Atiku, Muhammad Atiku Abubakar, a cikin jirgi jim kadan bayan da su ka dawo daga kasashen waje, inda a ka tabbatar da dan Atikun na dauke da cutar, kuma daga bisani shi ma Gwamnan Bauchi, hukumar ta NCDC ta tabbatar ya na dauke da kwayar cutar a halin da a ke ciki yanzu.
A cewar sanarwar da Muktar din ya fitar a jiya; “mu na sanar da illahirin jama’a cewar sakamakon gwajin da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, ta yi wa mutum shida ciki har da Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, iyalansa da mukarrabansa da su ka yi ma sa rakiya zuwa Legas sakamkon gwajin ya fito.
“Daga cikin shida da a ka gwada kan cutar, daya an tabbatar ya na dauke da cutar ta Covid 19, kuma wanda sakamakon gwajin ya tabbatar ya na dauke da cutar shi ne Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, wanda shi ne Gwamnan Jihar Bauchi.”
Muktar Gidado ya kara da cewa, a yanzu haka gwamnan ya na killace, inda likitocinsa ke duba shi da kuma jami’an hukumar NCDC da su ke sanya ido a kan lafiyarsa.
“Gwamnan ya na bukatar addu’o’i na musamman daga jama’a, sannan ya na kuma neman dukkanin wanda ya yi mu’amala da su ko wadanda su ke jin wani nau’i na rashin lafiya da su gaggauta kai kansu ga jami’an kiwon lafiya, domin yin gwaji na musamman, domn kare yaduwar cutar ta Covid 19,” a cewar sanarwar.
Da ya ke yi wa manema labarai karin haske kan halin da gwamna ke ciki a halin da a ke ciki, kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Maigoro, ya shaida cewar har zuwa yanzu jikin gwamnan bai tsananta ba, inda ya ce gwamnan ya na karkashin kulawarsu na likitoci tare da sanya idon hukumar NCDC.
Dakta Maigoro ya tabbatar da cewar yanzu haka jihar Bauci ta shiga jerin jihohin da a ka tabbatar su na dauke da cutar, sai ya bayyana cewar mutum guda wanda shi ne gwamnan jihar an tabbatar ya na dauke da cutar, sai ya kara da cewa yanzu haka babu wani da su ke zargi ya na dauke da cutar baya ga gwamnan, sai dai ya ce sun sauke daukar samfurin wasu mutane kusan 15 da su ka kai NCDC domin gwaji da tabbatar da matakin halin lafiyarsu.
A cewar Maigoro; “Bauchi yanzu ta shiga jerin wadanda su ke da wannan ciwon na Covid 19. Mu na da kes guda daya da aka tabbatar, ba mu da wani kuma da muke zargi yana da cutar kawo yanzu, amma muna jiran sakamakon gwajin wasu da aka dauka da aka kai. Idan kuna biye da alkaluma a Nijeriya akwai mutum 42 da suka kamu da cutar, a cikin 42 din akwai 1 a jihar Bauchi wanda kuma shine gwamnan jihar Bauchi,”
Ya ce, sun dauki gwajin jina na makusantan gwamna su 15 a halin da ake ciki domin gano ko suna dauke da cutar ko babu, sai dai ya ce ba zai bayyana wane da wane bane suka dauki jininsu, amma dai ya ce suna jiran sakamakon wasu karin mutum 15 da suka yi mu’amala da gwamnan.
Dangane da batun wadanda suka yi mu’amala da gwamna kuwa, ya shaida cewar mataki-mataki ne na mu’amala akwai wanda ba ma a tsammanin daga irin wannan mu’amalar mutum na dauke da cutar, “Dukkanin wadanda yayi mu’amala da su muna ta kan bincike sannu a hankali, su ma NCDC suna nasu binciken kama daga wadanda yayi mu’amala da su a Abuja da Bauchi. Mataki biyu ne, akwai wadanda suka yi mu’amala da su da ya dace ne kawai su killace kansu, wasu kuma jininsu za mu dauka, amma su wadanda suke kaiwa matakin yin mu’amala da shi da har sai an gwada jininsu mu’amalarsu daban ne, amma duk muna bin komai a kimiyyance duk wadanda yayi mu’amala da su muna kan tantancewa,” A cewar Kwamishinan.
Dakta Maigoro ya daura da cewa, “Gwamna yana killace ne a muhallin da muke bashi magani a nan jihar Bauchi, mu na kuma iya kokarinmu wajen ba shi magani, NCDC su na kan kokarin dafa mana da yanda za a shawo kan komai. A halin da ake ciki gwamna yana nan cikin koshin lafiya, bayan kwana kadan zai cika adadin sati biyu da mu’amalarsa da shi dan Atiku, za a sake daukan jininsa a sake dubawa mu na kuma ba shi magani, idan an sake kai gwajin jinsa za a sake samun sakamako,” a cewar shi.
Dakta Maigoro ya kara da cewa dukanin alamun cutar na mura, kasalar jiki, zazzabi da tari duk baya yinsu a halin yanzu, sai ya tabbatar da cewar dukkanin magani za su ci gaba da bashi.
Da ya ke tusa jawabin, shugaban hukumar lafiya a matakin farko na Jihar, Dakta Rilwanu Muhammad ya shaida cewar dole ne sai jama’an jihar sun ba su hadin kai wajen kare kai daga cutar, inda ya ce akwai gabar da za su bi domin tabbatar da jama’an jihar sun bi dukkanin matakan da su ka gindaya mu su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: