Connect with us

NOMA

Yadda Manoma Za Su Samu Kudi A Noman Agwaluma

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yunkuro wajen daukaka noman Agwaluma a tsakanin kananan manoma dake kasar nan da kuma masu sarrafa ta din su samu kudade da yawa daga nomanta.

Agwaluma wacce akafi sani a turance da ‘bolatile oils’ ta na dauke da sanadari da dama, har ila yau, Agwaluma ta kasance bawai ta na dauke da mai bane tana kuma dauke da ruwa a jikinta gaurare da mai.
kwararru sunyi amannar cewa, idan aka baiwa fannin noman Agwalumar mahimmancin da ya dace, a cikin sauki manoman zasu iya noman ta, inda kuma daga nan, masu sarrafa Agwalumar zasu iya sarrafa man dake a jikinta.
Masana’antun dake sarrafa amfanin gina suna yin amfani da Agwalubar wajen sarrafa abinci da iri-iri, musamman sarrafa Biskit, Alewa, Kek da sauran su.
Bugu da kari, ana kuma masana’antu suna yin amfani da Agwalumar, musamman wajen sarrafa Lemin Kwalba a natsayin kayan kanshi da kara kuzari ga dan adam, inda kuma ta kasance masana’antun suna yin amfani da ita wajen sarrafa kayan kwaliyar mata kamar su jan baki, man shafawa da sauran su.
Wani kundi da ya fito daga Cibiyar gudanar da bincike da samar da ci gaban kaya RMRDC ta sanar da cewa, tana sin ta shigo da tsarin ‘HS Code 33’ bisa ga bukatar da masana’antun kasar nan suke dashi.
Darakta Janar na Cibiyar ta RMRDC Farfesa Ibrahim Hussaini Doko ne ya sanar da hakan, inda kuma Darakta Janar na Cibiyar Farfesa Ibrahim Hussaini Doko ya ci gaba da cewa, daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2017, an kashe naira 61,067,925.00 wajen shigo da wani sanadarin Agwaluma daga kasar waje da kuma kashe naira 72,574,109.00 wajen shigo da sanadarin lemon oil duka tsakanin shekarun.
A cewar Darakta Janar na Cibiyar ta RMRDC Farfesa Ibrahim Hussaini Doko, sauran ire-irenn na Agwalumar da ake shigo dasu cikin kasar nan sun hada da na Mentha oil, da ta kai naira 222,655,364.00, sai Mints oil data kai naira 22,154, 035, Citronella oils, naira 54,665,373.00, Resinoids, naira 182,292,905.00, Akueous kimanin naira 566,523,760.00.
Darakta Janar na Cibiyar ta RMRDC Farfesa Ibrahim Hussaini Doko ya ci gaba da cewa, hakan ya kuma a zahairi na irin bukatar da ake da ita na zuba jari a fannin nomanta a kasar nan, inda Farfesa Doko duk da yawan fadin kasar noma da kasar nan take dashi don noma Agwalumar sama da kashi 95 a cikin dari na Agwalumar ake da bukata a cikin gida ana shigo da ita ne daga waje.
A karshe, Darakta Janar na Cibiyar of the Farfesa Ibrahim Hussaini Doko, ya sanar da cewa, hakan ta kuma janyo rashin samar da ci gaba na samar da kayan da za’a arrfa su, hada su agu daya da kuma sayar da Agwalumar a kasar nan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: